Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano
Published: 1st, October 2025 GMT
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba.
“Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo.
“A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa a ajiye duk zarge-zargen da ba su da hujja, yayin da muka rubuta waɗanda aka tabbatar da hujja a kansu.
“Hatta wuraren da ya tsaya ko ya yi jinkiri a cikin bidiyon mun rubuta a cikin rahoton,” in ji kwamitin.
Kwamitin ya ƙara da cewa za a tura masa takarda domin ya zo ya kare kansa, kafin daga bisani a aika da shawarwari ga gwamnati don ɗaukar mataki.
“Za a fitar da takardar kiransa, kuma kafin ya kare kansa, an dakatar da shi daga dukkanin wasu ayyukan koyarwa da wa’azi.
“Bayan ya yi bayaninsa, kwamitin zai gabatar da rahoto da shawarwari ga gwamnati domin ɗaukar mataki na gaba. Za a gayyace shi nan gaba kaɗan, kuma za a ba shi isasshen lokaci ya bayyana,” in ji Sagagi.
Ya ce dakatarwar ta zama dole domin Malam Lawan ya samu damar zuwa gaban kwamitin ya kare kansa kan zarge-zargen yin kalaman da ake ganin na ɓatanci ne ga Manzon Allah (SAW).
Sagagi, ya ce har sai an kammala bincike da jin ta bakin Malam Lawan ne, za a yanke hukunci na gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɓatanci dakatarwa Kwamitin Shura Malam Lawan Triump zargi Malam Lawan
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ƙara kula da tsaro tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, yayin da ’yan bindiga suka fara kai hare-hare a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina.
Sarkin, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar Faruruwa da ke Ƙaramar Hukumar Shanono a Jihar Kano.
Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16 Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — MuftwangA baya-bayan nan ’yan bindiga sun kai hari yankunan, inda suka sace shanu tare da yin garkuwa da mutane.
Sarki Sanusi, ya ce yawan hare-haren da ake fuskanta a yankin ya nuna cewa ana buƙatar kula da goyon bayan sarakunan gargajiya, gwamnati da kuma ƙungiyoyin sa-kai.
“Tsawon watanni da suka gabata, hare-hare sun ƙaru a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina, inda ’yan bindiga ke zuwa su sace shanu, su kashe jama’a, su yi garkuwa da maza da mata,” in ji shi.
Ya ce ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mazauna yankin da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da goyon bayan gwamnati, da kuma ƙarfafa musu gwiwa su taka rawa wajen kare ƙauyukansu.
“Nauyinmu ne a matsayinmu na shugabanni mu zo mu ga mutanenmu, mu yi musu ta’aziyya, mu kuma tabbatar musu cewa gwamnati da jami’an tsaro suna yin iya bakin ƙoƙarinsu,” ya ce.
Sarkin ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta tura jami’an tsaro da kayan aiki don tsaron yankin.
“Gwamna ya sayi motocin aiki, ya samar da kayan aiki, kuma mutane na gani da idonsu yadda sojoji da ’yan sanda ke yawan sintiri a yankin.
“Muna kuma ƙarfafa musu gwiwa su yi amfani da ’yan sa-kai wajen kare ƙauyukansu,” a cewarsa.
Sarki Sanusi, ya kuma bukaci al’ummomin Katsina da ke maƙwabtaka da yankunan da su tabbatar cewa yarjejeniyar sulhu da suke yi da ’yan bindiga ba za ta zama silar kawowa Kano hari ba.
Ya yi addu’ar Allah Ya wanzae da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa, tare da alƙawarin ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar domin kare rayukan jama’a.
“Muna rokon Allah Ya dawo mana da zaman lafiya, kuma za mu ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinmu tare da gwamnati domin tabbatar da tsaro a wannan jiha,” in ji shi.