Zargin Ɓatanci: Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano
Published: 1st, October 2025 GMT
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba.
“Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo.
“A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa a ajiye duk zarge-zargen da ba su da hujja, yayin da muka rubuta waɗanda aka tabbatar da hujja a kansu.
“Hatta wuraren da ya tsaya ko ya yi jinkiri a cikin bidiyon mun rubuta a cikin rahoton,” in ji kwamitin.
Kwamitin ya ƙara da cewa za a tura masa takarda domin ya zo ya kare kansa, kafin daga bisani a aika da shawarwari ga gwamnati don ɗaukar mataki.
“Za a fitar da takardar kiransa, kuma kafin ya kare kansa, an dakatar da shi daga dukkanin wasu ayyukan koyarwa da wa’azi.
“Bayan ya yi bayaninsa, kwamitin zai gabatar da rahoto da shawarwari ga gwamnati domin ɗaukar mataki na gaba. Za a gayyace shi nan gaba kaɗan, kuma za a ba shi isasshen lokaci ya bayyana,” in ji Sagagi.
Ya ce dakatarwar ta zama dole domin Malam Lawan ya samu damar zuwa gaban kwamitin ya kare kansa kan zarge-zargen yin kalaman da ake ganin na ɓatanci ne ga Manzon Allah (SAW).
Sagagi, ya ce har sai an kammala bincike da jin ta bakin Malam Lawan ne, za a yanke hukunci na gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɓatanci dakatarwa Kwamitin Shura Malam Lawan Triump zargi Malam Lawan
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO).
Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA