Majalisar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi Naira biliyan 75
Published: 25th, September 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na Naira biliyan 75 na kasafin kuɗin jihar da ƙananan hukumomi.
An amince da kasafin kuɗin ya zama doka ne a yayin zaman majalisar wanda mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Sani Isiya ya jagoranta.
Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a Filato An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna ZulumMatakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar wanda Hon Ibrahim Hamza Adamu ya gabatar.
Ƙarin kasafin kuɗin da aka amince da shi ya ƙunshi Naira biliyan 58 na Gwamnatin Jiha da kuma Naira biliyan 17 na Ƙananan Hukumomi 27, wanda ya ƙunshi kashe kuɗaɗe na yau da kullum da na manyan ayyuka.
A cikin jawabinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar ya bayyana cewa, bisa wata wasiƙa da aka samu daga ɓangaren zartarwa, an yi shirin ƙarin kasafin ne domin magance matsalolin kuɗi da suka kunno kai.
Yin hakan zai haɓaka ayyuka da shirye-shiryen da ke gudana a cikin fannoni masu mahimmanci kamar: ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa da noma.
Majalisar dai ta amince da ƙarin kasafin kuɗin na shekarar 2025, wanda ya kai Naira biliyan 689.3 kuma majalisar ta amince da shi tun a ranar 31 ga Disamba, 2024.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jigawa Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ƙarin kasafin Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.
Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.
Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.