Aminiya:
2025-09-24@22:56:32 GMT

Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko cikin kusan shekaru 60

Published: 25th, September 2025 GMT

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya.

Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD.

Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe

Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981.

Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya ɗaiɗaita Syria, amma ya alƙawarta gudanar da zaɓuka a ƙasar.

Jawabin da ya yi a taron na MDD da ke gudana a New York ya ɗauki hankalin mahalarta taron a Amurka, ƙasar da a baya ta sanya tukwicin dala miliyan 10 ga wanda ya taimaka aka kama shi.

A watan Disamban da ya gabata ne aka kawo ƙarshen mulkin kama-karya da iyalan Assad suka shafe kusan rabin ƙarni suna yi a Siriya, bayan da aka kifar da Shugaba Bashar al-Assad a wani gagarumin samame da dakarun ’yan tawaye ƙarƙashin jagorancin al-Sharaa suka kai.

Kifewar Assad ta kawo ƙarshen daular mulkin da ta mamaye Siriya na tsawon shekaru 50, tare da kawo ƙarshen yaƙin basasa da ya shafe fiye da shekaru 14 yana addabar ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bashar al Assad Syria ya yi jawabi a

এছাড়াও পড়ুন:

Xinjiang A Shekaru 70: Yadda Yankin Ya Habaka Da Aikin Noma

A yau, jihar Xinjiang tana bikin cika shekaru 70 da kafuwa cikin alfahari da kuma kyakkyawar manufa. Sauye-sauyen aikin gona a yankin suna nuna juriyar mutanensa da karfin hangen nesa yayin da karfin tattalin arzikinsa ya zuwa tsakiyar 2025, ya kai kudin Sin fiye da yuan tiriliyan 9.84 (kwatankwacin dala tiriliyan 1.35), bisa samun ci gaba da kaso 5.7 a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xinjiang A Shekaru 70: Yadda Yankin Ya Habaka Da Aikin Noma
  • Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe
  • Xi Ya Halarci Nune-Nune Game Da Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Jihar Xinjiang 
  • Imam Sayyid Ayatollah Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo
  • Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • Kashim Shettima Ya Isa New York Halartar Taron UNGA Na 80