Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba
Published: 23rd, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya shiga jirgi zuwa birnin NewYork a safiyar yau talata.
Sannan gaskiya mai dacin da ke faruwa a halin yanzu shi yadda yara da jarirai da suke mutuwa a gaza, a kisan kiyashin da HKI take aiwatarwa a Gaza kimani shekaru 2 da suka gabata. Sannan yayi allawadai da kasashen da suke goyon bayan wannan Haramtacciyar kasar kan abinda take yi a Gaza.
Ya ce bai sani ba, shin suna bukatar dukkan duniya su taru suka gasa guda mai karfi a duniya suke nufi ne, ? Ai kasashen duniya suna da damar amfani da arzikin da All…ya basu.
Shugaban Pezeshkiyan ya salalami Jagoran Juyin juya Halin musulunci kafin ya wuce zuwa NewYork
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida September 23, 2025 Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah September 23, 2025 ‘Yan Gwagwarmaya Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza September 23, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025 Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Kashi 81.8 cikin 100 kuma sun bayyana cewa, “kafa kasa mai cin gashin kanta, mai cikakken ‘yanci ta Falasdinu bisa kan iyakokin da aka shata a shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta” ta zama wata matsaya da aka cimma a tsakanin kasashen duniya.
A cewar bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na Gaza, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane 65,283 tare da jikkata wasu 166,575 tun bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinu a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023. A kuri’ar jin ra’ayoyin, kashi 90.8 cikin 100 na wadanda suka yi Allah-wadai da ta’asar da Isra’ila ke tafkawa, kuma sun yi imanin cewa, ya kamata Isra’ila ta gaggauta dakatar da hare-harenta na soji a zirin Gaza. Kazalika, kashi 92.1 cikin 100 sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki tare da yin taron dangi wajen taka birki ga farmakin sojojin Isra’ila a Gaza. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp