INEC ta amince da jam’iyyar haɗaka ta ADC
Published: 10th, September 2025 GMT
Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.
Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli.
Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa.
Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a jerin rukunin shugabannin jam’iyyun da ta aminta da su ba a hukumance.
Sauran shugabannin da sunayensu suka bayyana a jerin da hukumar ta fitar sun haɗa da: Ibrahim Ahmad Mani — Ma’aji, Akibu Dalhatu — Sakataren kuɗi, da kuma Oserheimen Osunbor — mai bayar da shawara kan harkokin shari’a
Gamayyar ’yan adawar a Nijeriya sun haɗe a jam’iyyar ADC ne domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.
Bayan hawa kan mulki, Tinubu ya ɗauki manyan matakai da dama waɗanda suka sauya rayuwar al’ummar ƙasar, kamar cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a fannin kuɗi.
A halin yanzu dai, mafi yawan manyan jam’iyyun siyasa na ƙasar na fama da rikicin cikin gida, inda suke zargin jam’iyyar APC mai mulki da yi musu zagon ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: David Mark
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria