Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas
Published: 13th, September 2025 GMT
Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta kan mutane a unguwar Yaba, da ke Jihar Legas.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ginin ya rufta ne da misalin ƙarfe 8 na dare.
Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800 HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a KanoShaidu sun ce akwai mutane biyar zuwa shida a cikin ginin lokacin da abin ya faru.
NEMA ta ce ta ceto mutum huɗu, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.
Sai dai hukumar ta ce ba a tabbatar da adadin waɗanda har yanzu suke ƙarƙashin ginin ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ruftawa
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Ukuwannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan