Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240
Published: 24th, September 2025 GMT
Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025.
Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240).
Sabuwar motar ta 2025 na dauke da sabon fasali mai ban sha’awa da kuma Zubin da ya sa ta fi tsofaffin nau’ikan da suka gabace ta inganci.
A wani bidiyo da Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, an ga lokacin da ya karbi motar, inda ya bayyana cewa ya musanya tsohuwar motarsa tare da ƙarin kuɗi don samun wannan sabuwar sigar.
“Da farko, sai da muka muka cika kudi kafin mu karbo wannan sabuwar. Na fi so matata ta samu abu mafi inganci,” in ji shi.
Lokacin da ya mika motar ga Chioma, ta bayyana cikin farin ciki matuka, yayin da Davido ke murna da ita yana cewa, “Mu ne 2025!”
Wannan kyauta ta zo ne makonni kadan bayan Davido da Chioma sun kammala jerin bukukuwan aure masu kayatarwa da suka ja hankalin duniya.
Auren na turawa da aka yi a Miami a ranar 10 ga Agusta, 2025, ya kasance babban abin kallo, inda aka kiyasta kashe kusan Dala miliyan 3.7 yayin gudanar da shi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai.
A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance.
Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Najeriya.