HausaTv:
2025-11-27@21:13:34 GMT

Kasashen duniya na yabawa Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump

Published: 4th, October 2025 GMT

Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump.

Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta ya ce ” Qatar na maraba da sanarwar da Hamas ta yi cewa ta amince da shirin na Shugaba Trump.

A nata bangare Masar tana kallon wannan a matsayin “ci gaba mai kyau.” Kuma tana fatan a sakamakon haka, bangarorin biyu “za su himmatu wajen aiwatar da shirin Shugaba Trump da kuma kawo karshen yakin,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a shafin Facebook.

Ita ma Turkiyya a cikin wani sakon da ta fitar a shafin ‘’X’’, ta bayyana lamarin a matsayin wata “dama ta samar da tsagaita bude wuta nan take a Gaza da kuma kai agajin jin kai ga yankin da kuma bude hanyar samun ci gaba wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.”

A Turai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi bukaci sakin mutanen da ake garkuwa da su da kuma tsagaita bude wuta.

A nasa bangaren Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya bayyana amincewar Hamas da shirin na Trump a matsayin wani muhimmin ci gaba da ke ” kusanci da zaman lafiya fiye da kowane lokaci.”

Shi kuwa Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, a cewar mai magana da yawunsa, ya samu kwarin gwiwa game da matakin da Hamas ta dauka kan shirin na shugaban Amurka, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen wannan mummunan rikici a Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : Ana ci gaba da tir da Isra’ila kan kai farmaki akan jiragen ruwan agaji October 4, 2025 Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “ October 4, 2025 Washington Ta Bada Dalar Amurka Miliyon 230 Don Kwace Damarar Hizbullah October 3, 2025 Mutane 5 Sun Mutu Bayan Hari Kan Wurin Bautar Yahudawa A London October 3, 2025 Iran: Larijani Ya Yi Tir Da Kasashen Yamma A Kokarin Tursasawa Iran October 3, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adam Sun Nuna Damuwarsu Da Halin Wadanda HKI Ta Tsare October 3, 2025 Kasar Beljium Ta Ce Bata Amince A Yi Amfani Da Kudaden Rasha Don Yaki Da Ita A Ukraine Ba October 3, 2025 Jam’iyyar PPRD Ta yi Tir Da Hukuncin Kisa Da Aka Yankewa Kabila Na Congo October 3, 2025 Iran: Mas’ud Pezeshkiyan Ya Isa Birnin Bandar Abbas Dake Kudancin Kasar October 3, 2025 Adadin Falasdinawa Da Suka Rasu Sakamon Harin Isra’ila A Gaza 66225. October 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin

Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin  ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.

Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.

A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.

 A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa  Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.

Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.

Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare   November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya
  • Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar