A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.

Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya.

“Tare, dole ne mu yi adawa da manufofin da ke ƙoƙarin ƙara talauci ga ƴan ƙasa da ɗora mana nauyin nan gaba. Lamarin ya isa haka. Ƴan Nijeriya na da haƙƙin samun sassauci ga lamarin da shafi tattalin arziƙi, ba a ci gaba da azabtar da su ba.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnonin Ƙwadago

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote

Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa.

Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko.

“A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi.

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Ya ci gaba da cewa, “Amma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya su yi alfahari.”

Ɗangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa ƙasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen ƙarfi wajen cika buƙatar cikin gida.

Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.

Ɗangote ya ƙara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faɗin ƙasar, rage farashin zai fi tasiri.

Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.

“Ba mu kore kowa daga aiki ba, sai dai muna ƙara samar da ayyuka,” in ji shi.

Ɗangote ya zargi masu harkar mai da haɗa kai da ’yan kasuwa na cikin gida da na waje da ƙoƙarin hana nasarar matatar.

“Yadda aka hallaka masana’antar yadi, haka suke ƙoƙarin kashe matatar mu,” in ji shi.

A kan zargin cewa bai wadatar da ƙasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: “Idan ba mu da ƙarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa ƙasashen waje?”

Ya kuma yi ba’a ga Ƙungiyar Ma’aikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote “kyautar Girka ce.” Dangote ya ce: “Ko da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.”

Ya jaddada cewa abin da Najeriya ke buƙata yanzu shi ne kare masana’antunta, domin ci-gaban tattalin arziki da kuma rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa