Aminiya:
2025-07-07@14:02:09 GMT

Wata bas kirar Macarpollo dauke da mutane da yi hatsari a Jos

Published: 7th, July 2025 GMT

Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato.

Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita.

Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari Macarpollo motar

এছাড়াও পড়ুন:

Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza

Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi.

Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza.

Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno

TRT ya ruwaito cewa an gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra’ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi ya magance damuwar da ya shiga.

“Ba zai iya jurewa ba kuma ya koka da ganin hotunan gawawwaki da kuma jin warin mutuwa a kullum,” in ji mahaifiyarsa.

A cewar kafafen yaɗa labarai na Isra’ila, adadin sojojin da suka kashe kansu ya ƙaru tun bayan ɓarkewar yakin Gaza a watan Oktoban 2023.

Wani rahoto daga jaridar Israel Hayom ya nuna cewa sojoji 21 sun kashe kansu a shekarar 2024.

A watan Mayu, jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ce sojoji 42 sun kashe kansu tun bayan ɓarkewar yakin Gaza.

Duk da kiran duniya na tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza, inda ta kashe fiye da mutum 57,400, yawancinsu mata da yara, tun daga watan Oktoban 2023.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza
  • Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos
  • Mutane 21 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano
  •  Togo: An Yi Kiran Sake Yin Wata Sabuwar Zanga-zanagr Kin Jinin Gwamnati
  • Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
  • Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
  • Tsoro, Fargaba Da Wahala: ‘Bala’in Da Muka Gani A Yakin Sudan
  • Akalla Mutane 52 Suka Rasa Rayukansu Saboda Ambaliyan Ruwan Sama A Jihar Texas Na Kasar Amurka
  • Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung