An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai.

Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.” Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar duniya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Farashi

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu

Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009.

An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri

A cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini.

Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin Iraki, tare da goyon bayan amfani da na’urorin leƙen asiri da bincike mai tsanani a matsayin martani ga harin ta’addanci na ranar 11 ga Satumba, 2001.

Bayan ya bar ofis, Cheney ya zama ɗaya daga cikin masu sukar salon jagorancin shugaban ƙasa Donald Trump a wa’adin mulkinsa na farko, musamman bayan ’yarsa, Liz Cheney, ta zama jigo cikin ’yan jam’iyyar Republican da suka fito fili suna sukar Trump, lamarin da ya zamo sila dakatar da shi daga jam’iyyar.

Liz Cheney ta kasance ɗaya daga cikin ’yan jam’iyyar da suka soki matakin magoya bayan Trump na tayar da tarzoma a ginin Majalisar Dokoki ta ƙasar (Capitol) bayan shan kaye a zaɓen ranar 6 ga Janairu, 2021.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
  • Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu
  • Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
  • Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 
  • Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
  • Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka