Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku.

Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na 0.

5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensu, daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS).

A cikin wata sanarwa haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da kudaden ne don tafiyar da al-amuran ƙungiyar.

Harajin, wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani kaya da za a shigo da su daga ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS da za su shigo ƙasashen uku.

Wannan sabuwar doka dai, ta ci karo da yunƙurin da ƙungiyar ECOWAS ke yi na bai wa ƙasashen da ke ƙungiyarta da ma ta  AES damar shigar da kaya ba tare da shinge ba,  duk kuwa da ficewar ƙasashen uku daga ƙungiyar a watan Janairun da ya gabata.

ECOWAS dai ta tabbatar da ci gaba da ba wa, kayakin da ake shigo da su daga ƙasashen uku damar wucewa ba tare da shinge ba kamar yadda tsarin cinikayya da zuba jari na ƙungiyar (ETLS) ya tanada.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.

M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.

Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”

Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.

Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.

Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon
  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje