Jigawa Za Ta Kafa Kananan Bankuna 5 A Wasu Sassan Jihar
Published: 25th, September 2025 GMT
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta amince da fara shirin karbar lasisin aiki don kafa sabbin Kananan bankunan guda 5 a wasu wurare da aka zaba a fadin jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.
A cewarsa, shirin wani bangare ne na dabarun gwamnatin jihar na fadada hanyoyin samar da kudade da zurfafa shiga harkokin tattalin arziki a yankunan karkara da marasa galihu.
Ya bayyana cewa, za a kafa bankunan masu karamin karfi a kananan hukumomin Birniwa, Gujungu – Taura, Guri, Gwaram da Kaugama.
Ya ce, shawarar da majalisar ta yanke ya nuna irin sadaukarwar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta yi na bunkasa hada-hadar kudi a matsayin wani makami na rage radadin talauci, bunkasa sana’o’in cikin gida, da karfafa tattalin arziki daga tushe.
Sagir ya ci gaba da cewa, sabon tallafin kudi na da nufin karawa kananan bankunan jihar tallafi, da samar da ayyuka na kudi kamar tanadi, bashi, da tallafin kananan ‘yan kasuwa ga daidaikun jama’a da al’ummomin da a al’adance ke cire su daga tsarin banki na zamani.
Ya kuma bayyana cewa, majalisar ta kuma amince da bayar da kwangilar samar da lantarki ta amfani da hasken rana a muhimman cibiyoyin zamantakewar al’umma a jihar.
Ya ce, darajar kwangilar ta kai sama da naira miliyan 733, inda ya kara da cewa amincewar ya yi daidai da manufofin shirin samar da hanyoyin samar da hasken rana na jihar, wanda aka tsara shi don fadada wutar lantarki zuwa sassa masu muhimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya, da sauran muhimman ababen more rayuwa a fadin Najeriya.
Kwamishinan ya ce, tsarin tantancewar fasaha da tsare-tsare zai samar da cikakken tantance bukatun makamashi, dacewa da kayayyakin more rayuwa, da kuma tsare-tsaren aiwatar da aikin shimfida tsarin hasken rana a zababbun makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, da sauran muhimman cibiyoyin gwamnati a fadin jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, aikin na nuni da yadda gwamnatin Namadi ta kuduri aniyar samar da hanyoyin samar da makamashi mai dorewa, da samar da ababen more rayuwa masu jure yanayi, da kuma inganta ayyukan hidima a sassa masu muhimmanci.
KARSHE/USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন: