Aminiya:
2025-09-24@08:34:05 GMT

Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe

Published: 21st, September 2025 GMT

Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin.

An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon.

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro

Shugaban ya ce shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na bunƙasa kiwon lafiya a matakin farko, musamman ga mata masu juna biyu daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa.

Ya kuma bayyana cewa an fara gwajin jini kyauta ga mata masu juna biyu a dukkanin cibiyoyin haihuwa, domin gano matsalolin lafiya tun da wuri.

Wasu daga cikin matan da suka amfana sun gode wa gwamnati, inda suka bayyana cewa shirin zai rage musu kashe kuɗi tare da tabbatar da lafiyarsu da ta jariransu.

Wata mata mai suna Sa’adatu Garba, ta bayyana jin daɗinta game rabon kayan.

“Wannan kaya da aka ba mu tabbas za su taimaka, musamman duba da halin matsi da ake ciki,” in ji ta.

Ita kuwa Rabi Mustapha cewa ta yi: “Wannan babban tagomashi ne, muna godiya Allah Ya saka da alheri. Wannan shiri zai sauƙaƙa mana wajen rage kashe kuɗaɗe.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ƙaramar Hukumar Gombe lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Bankin Nijeriya Ya Rage Kuɗin Ruwan Da Bankuna Ke Caja

 

Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.

 

Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana samu a jere.

 

Tuni, dama masana suka yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.

 

Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Bankin Nijeriya Ya Rage Kuɗin Ruwan Da Bankuna Ke Caja
  • CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake Da Mata 2 A Filato
  • APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata
  • Mata Ne Ƙashin Bayan Gyaran Duk Wata Al’umma, In Ji  Sheik Shamsudeen