Kasashen Duniya Suna Yin Gargadin Cewa HKI Za Ta Kai Wa Jiragen Ruwan Ceto Na “Sumdu” Hari
Published: 25th, September 2025 GMT
Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila tana shirin kai musu hari.
Jiragen ruwan dake son kawo karshen killace sun kai 50, suna kuma dauke da kayan agaji
HKI ta aike da jiragen sama marasa matuki wadanda suke yin shawagi na tsokana a samansu da kuma watsa musu wasu sanadarori masu guba.
A jiya da dare jiragen ruwan su ka bar gabar ruwan ‘ Girka su ka shiga iyakokin ruwan kasa da kasa da zai nausa ya nufi gabar ruwan Gaza.
A gefe daya, ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da jirgin yaki na biyu wanda zai rika bin bayan jirgin ruwan na ceto.
A gefe daya, wadanda suke cikin jirgin ruwan Agaji na “Umar Mukhtar” wanda ya taso daga kasar Libya da zummar hadewa da na “Sumud” sun bayyana cewa, a jiya Laraba wasu kananan jiragen sama marasa matuki 3 sun rika yin shawagi a samansu. Sun kuma kara da cewa har yanzu suna ci gaba da iyo a cikin ruwan domin hadewa da babban jirgin ruwan ” Sumud”.
Kwakanin kadan da su ka gabata ne dai kasar Libya ta sanar da cewa, za ta aike da jirgin sama mai saukar angulu domin ya rika yi wa jirgin na “Umar Mukhtar” rakiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka September 25, 2025 Iran Za Ta Rika Samar Da Megawatti 5000 Daga Tashar Nukiliya Ta Bushehr September 25, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Shugaban Faransa A Gefe Taron M D D. September 25, 2025 Spain Ta Aike Da Jirgin Ruwan Don Taimakawa Tawagar Flotilla Zuwa Gaza. September 25, 2025 Kuwait Ta Bayyana Halin Da Ake Ciki A Gaza A Matsayin Babban Bala’i. September 25, 2025 An Jikkata Yahudawa 22 Bayan Harin Da Dakarun Yamen Suka Kai A Eilat. September 25, 2025 Shugaban Iran:Wadanda Suka Fice Daga Yarjejeniyar JCPOA Ke Da Alhakin Halin Da Ake Ciki. September 25, 2025 Shugaban Colombia ya bukaci a kafa kawancen soji domin ‘yanto Falasdinu September 24, 2025 Rasha ta mayar wa da Trump martani kan yakin Ukraine September 24, 2025 Pezeshkian : Hare-haren watan Yuni kan Iran cin amanar diflomasiyya ne September 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jirgin ruwan
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata.
Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum.
Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran bukatun yau da kullum.
Yace ana samun ribar kimanin naira dubu goma zuwa ashirin a kowace rana daga siyar da kifin ga matafiya da kuma baki masu kai ziyara garin.
A don haka, Umar yayi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta yi yashen madatsar ruwan saboda a samu karin kifaye da kuma ruwa da za a iya amfani da shi domin noman rani.
Shi ma a yayin tattaunawa da Dagacin Warwade, Malam Musa Ado, ya ce madatsar ruwan tana samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da hana tafiya zuwa cirani a sauran yankunan kasar nan da sunan yin sana’o’i.
Ya ce matasan yankin suna gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma nomar rani da ta damina.
Sai dai kuma, Malam Musa ya koka kan rashin samar da injinan noman rani da kuma Malaman gona kamar yadda ake yi a gwamnatocin baya.
Kazalika, yace a ‘yan kwanakin baya gwamnatin jihar Jigawa ta kai ziyara kauyen inda ta sanar da cewar Bankin duniya zai samar da wasu kudade ta hannun gwamnatin tarayya wanda za’a baiwa gwamnatocin jihohi domin yashewa tare da gina burtuloli da hanyoyin noman rani.
Bisa haka ne dagacin yayi kira ga gwamnatin jihar da ta fara yin garambawul a madatsar ruwan domin a baiwa mazauna yankunan damar amfani da shi.
A shekarun baya dai, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da irin kifaye guda dubu Dari uku domin inganta samar da kifi a yankin.
Usman Mohammed Zaria