Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu
Published: 29th, September 2025 GMT
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya.
Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar.
ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar KanoRahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi.
Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa.
Mahukunta sun tabbatar da rasuwar ɗalibar da aka bayyana a matsayin babban rashi ga iyalai, makusanta da al’ummar jami’ar.
Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na jami’ar, Alhaji Baba Akote, ya fitar, ya bayyana cewa ɗalibar tana da nutsuwa sannan mai hazaƙa ce da ladabi ga malamanta da kuma faran-faran a cikin ’yan uwanta ɗalibai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗaliba Jihar Neja
এছাড়াও পড়ুন:
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle
Har yanzu ba a saka ranar sauraron ƙarar ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA