Aminiya:
2025-09-24@08:34:22 GMT

Dalilin da muke goyon bayan tsare-tsaren Tinubu na karɓo bashi — Majalisar Wakilai

Published: 22nd, September 2025 GMT

Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan.

Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja.

Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja

Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa tushe da aka ƙirƙira da manufa ta yaudara.

A cewarsa, “kwanan nan, an yi wa jawabin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar ya gabatar a taron majalisun dokoki na Afirka (West African Parliamentary Conference, WAPC) mummunar fassara, har aka rika yi wa majalisar kuskuren fahimta cewar ba ta goyon bayan tsare-tsare da dabarun rancen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Wannan kuskuren fahimta ne, kuma ba gaskiya ba ce.”

Abbas ya jaddada cewa Majalisar Dokokin Tarayya baki ɗaya, sun amince cewa rance mai tsari cike da kulawa hanya ce da ake amfani da ita wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ƙarfafa ci gaban tattalin arziki, da kuma tallafa wa marasa galihu.

Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin jagorancin Tinubu, ana karkatar da kuɗaɗen rancen ne zuwa manyan ayyuka da suka haɗa da wutar lantarki, sufuri da noma, waɗanda za su ƙara inganta hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga.

Abbas ya kuma tabbatar da cewa duk wani bashi za a karɓo shi ne cikin hikima da kuma tsare-tsaren rance na ƙasar da wanda sun dace da duk wasu ƙa’idoji a fadin duniya.

Kazalika, ya jaddada muhimmancin kafa Ofishin Kasafin Kuɗi da Bincike na Majalisa (NABRO) domin yin bincike mai zaman kansa kan batutuwan rance, karɓo bashi da kuma manufofin kuɗi.

Sai dai shugaban majalisar ya yi gargaɗin cewa duk da yake karɓo rancen wajibi ne, amma buƙatar rufe ɓarakar sata da fitar da kuɗaɗen haramun ita ma babban lamari ne da ya zama tilas.

Ya bayyana cewa Najeriya na asarar kusan dala biliyan 18 duk shekara ta hanyar cin hanci da zamba da kuma halasta kuɗaɗen haramun — adadin da ya kai kusan kashi 3.8% na GDP.

Abbas ya ce haɗa rance mai tsari da kuma tsauraran matakan sa ido da yaƙi da cin hanci shi ne zai tabbatar da makomar tattalin arzikin Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nijeriya rance tsare tsare

এছাড়াও পড়ুন:

Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ribas, Fubara Ya Ziyarci Tinubu A Fadar Gwamnati A Abuja

A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe…

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa
  • Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata Natasha
  • An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
  • Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ribas, Fubara Ya Ziyarci Tinubu A Fadar Gwamnati A Abuja
  • Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai
  • Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
  • SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook