Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya.

A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli da dama, sun dabaibaye NPA da suka haɗa da, cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki, musamman na zamani da sauransu, inda waɗannan matsalolin suka haifar wa da NPA koma baya matuƙa, musamman na wajen zama a kan gaba wajen gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka.

Amma, za mu iya cewa, Allah san barka da naɗa Dakota Abubakar Ɗantsoho, a matsayin zaƙaurin shugaban hukumar kuma mai hangen nesa, wanda ya a baje ƙwarewarsa da kuma hazaƙarsa da su yi daidai da ƙugurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake farfaɗo da fatan ga ƴ an ƙasar da kuma ita ƙasar Kant’s, wato Renewed Hope Agenda.

Ɗantsoho, da shigarsa ofis, bai wani ɓata lokaci ba, ya fara da ƙaddamar da gagarumin bincke domin gano inda ake da giɓi kan gudanar da ayyukan a NPA wanda hakan ya ba shi damar, yin garanbawul baki ɗaya a hukumar, musamman domin ya sake ɗora ta, a kan turba, mai ɗorewa.

Domin tabbatar da ya daƙile ƙalubalen cunkoson musamman na Jiragen Ruwa da ke sauka, Ɗantsoho ya yi ƙoƙari wajen ganin, an yi nesa da hanyoyin  Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas da Tashoshin Jiragen Ruwa na Fatakwal da ta Onne da ta Warri da kuma ta Kalaba musamman duba da cewa, rashin ɗaukar wannnan matakin tun da farko a baya, ya haifar da cunkoso da ya kai kaso 90

Kazalika, baya ga magance wannan matsalar ta cunkoso da shugaban ya yi,hakan ya kuma sanya hada-hadar kasuwanci a yankunan da ke a nahiyar Afirka, ƙara tunbatsa.

Ɗantsoho, bai tsaya a nan ba,misali  saboda tsaikon da ake samu a Kogin Riba Neja, ya ƙirƙiro da aikin yashe hanyoyin ruwan, musamman domin a rage cunkoso da ake samu a Tashar Jiragen Ruwa ta Onitsha, wanda hakan ya taimaka wajen ci gaba amfana da albarkatun tattalin arziki.

Bugu da ƙari, saboda burin da ya ke da shi, musamman na zamantar ƙufurin ƙara ciyar da hukumar gaba, Ɗantsho ya tabbatar da an ware dala biliyan ɗaya domin a yiwa ginin Tashar Jiragen Ruwa ta Tincan Island da  ta Apapa da ta, Riɓers da ta Onne ta ta Warri da kuma ta garin Kalaba.

Asusun Bunƙasa Ayyuka wato RHIDF ne, ke tallawa wajen gudanar da waɗannan ayyukan wanda hakan ɗai ƙara taimaka wa wajen ƙara bunƙasa ɗuba hannun jari a fannin.

Hakazalika, a ƙarƙashin iya salon shugabanci na gari na Dakta Ɗantsoho ke ci gaba da gudanarwa, an samu raguwa cunkson Jiragen Ruwa da sauka a Tashshin da suka kai kaso  45.1 da kuma samun ƙaruwar shigo da Kwantainoni, da suka kai kaso 9.7 wanda hakan, ya ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci natuƙa.

Ɗantso ya kuma ƙirƙiro da tsarin yin amfani da na’urar  Electronic truck call-up wanda hakan, ya ƙara zamantar da ayyuka a Tashohin Jiragen Ruwan tare da kuma rage cunkoso, Jiragen Ruwa.

Ɗaukacin waɗannan ayyukan da Ɗantsoho ke gudanawar, sun zo ne, daidai da manufar gwamnatin shuigaba Bola Tinubu.

Shugaban na NPA ya kuma kasance a kan gaba wajen ganin an ƙaddamar da Tashin Tsayawar Jiragen Ruwa  na kan tudu, kamar dai, na gain Funtuwa, da ke a jihar Katsina, wnada an yi hakan ne, domin ƙara haɓaka fitar da kana da ba su shafi fannin Mai ba da kuma ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci.

Shirin aikin kashe dala biliyan ɗaya a Tashar Snake Island wanda za a ƙara faɗaɗa kadada 85 a cikin Tashar, an yi ne, bisa nufin gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a Tashar, wanda hakan zai kuma ƙara ɗaga darajar Nijeriya a fagne kasuwanci.

Ayyukan ci gaba da Ɗantsho ke ci gaba da samarwa a NPA, ba wai kawai nan ya tsaya ba, domin kuwa, a kwanan baya, an zaɓe shi ya zama shugaban ƙungiyar  kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA.

Wannan zaɓar ta sa, ta nuna a zahiri, irin tunbatsar da ficen da ƙasar nan ta yi a fagen na harkar sufurin Jiragen Ruwa, musamman a nahiyar Afirka

Har ila yau, Ɗantsho shugaba ne, da bai yin wasa da kula da walwalar da haƙƙoƙin ma’aiakatasa, musamman domin ya tabbatar da yaƙi cin hanci da rasahawa.

Duk dai a ci gaba da marawa tsarin shugaba Tinubu na ci gaba da ƙara tarawa ƙasar kuɗaɗen shiga, Ɗantsoho ya amince da kafa tsarin tara kuɗaɗe shiga na kai tsaye, a NPA ta hanyar yin haɗaka da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta ta ƙasa wato NIMAS da kuma hukumar Kwastam.

Wannan manufar, an yi ta ne, domin a tabbatar da ana bin diddigin tara kuɗaɗen shigar da kuma kula da su.

Ɗantsoho, ya kuma tabbatar da ana ƙara ƙarafafawa masu hada-hdar Jiragen Ruwa na ƙasar guiwa wanda kuma ya yi daidai da manufar gwamnatin ƙasar.

Burin da har zuwa yau Ɗantsoho ya sanya a gaba shi ne, ganin NPA ta tsarewa tsara, wajen ƙara samar da ci gaba ba wai kawai a tsakanin nahiyar Afirka ba, har a ma faɗin duniya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hada hadar kasuwanci Jiragen Ruwa ta nahiyar Afirka a tabbatar da Ɗantsoho ya wanda hakan

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

A cewarsa, jihar ta ba da fifiko wajen samar da kudade, kayayyakin more rayuwa, da kuma samun damar koyo tun bayan hawansa kujerar mulki.

 

Gwamnan ya kara da cewa, yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimin ’ya’ya mata, bayar da tallafin karatu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya taimaka wajen kawo sabon matsayi a jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada ‘Yancin Kasar Na Mayar Da Martani Kan Sabawa Doka
  • Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Shugaban Kasar Faransa
  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  • Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi
  • Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025
  •  Yahudawa Suna Ci Gaba Da Yin Hijira Zuwa Wajen HKI
  • Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato