IRGC: Duk Wani Sabon Kuskuren Abokan Gaba Zai Fuskanci Mayar Da Martani Mai Tsanani
Published: 21st, September 2025 GMT
A wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar a jiya Asabar ya ce; Abinda ya faru a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki na farko da na biyu, mayar da martanin Iran ya haifar da sakamako mai karfi wanda aiki ne na tsawon lokaci.
Haka nan kuma sanarwar ta ce, duk wani sabon kuskure da abokan gaba za su yi na kawo wa Iran hari, to jamhuriyar musulunci ta Iran za ta sami fifiko akansu a fagen daga, domin martaninta zai zama mai tsanani.
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun kuma bayyana makon tsaron kasa mai tsarki na tunawa da yake-yaken da aka kallafawa Iran, a matsayin daya daga cikin lokuta masu girman matsayi a Iran.
A cikin kwanakin nan ne dai ake shiga makon tsaron kasa da ake yi a kowace shekara wanda na bana ya cika shekaru 45 ana yi.
Bayanin na IRGC ya kuma ce; A tsawon wannan loakcin jamhuriyar musulunci ta Iran ta dauki darussa masu yawa daga abinda ya faru a baya da hakan ya ba ta damar kera makamai na kanta domin kare kanta daga masu wuce gona da iri. Abinda ya faru a yayin yakin tsaron kasa mai tsarki na kwanaki 12 ya fito fili wanda kuma duniya ta gan shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Israila Ta Kai Hari Kan Wata Mota A Kudancin Labanon September 21, 2025 Iran Za ta Iya Shawo Kan Duk Wani Takunkumi Da Aka Sanya Mata . September 21, 2025 Pakistan:Yarjejeniyar Tsaro Da Suka Kulla Da Saudiya Kamar Kawancen Tsaro Na Nato Ne. September 21, 2025 Matatar Mai Ta Dangote Ta Kawo Ƙarshen Dogon Layin Mai A Nijeriya September 21, 2025 Isara’ila Ta Kaddamar Da Shirin Iko Da Wasu Yankuna A Yammacin Kogin Jodan. September 21, 2025 Iran za ta katse hulda da IAEA idan aka maida mata takunkuman MDD September 20, 2025 Venezuela ta bukaci MDD ta binciki harin Amurka a yankin Caribbean September 20, 2025 Spain za ta hada kai da ICC kan binciken laifukan Isra’ila a Gaza September 20, 2025 Falasdinawa 47 sun yi shahada a Hare-haren Isra’ila September 20, 2025 Sudan: Rundunar Daukin Gaggawa ( R.S.F ) Ta Kashe Mutane 75 A Wani Hari Da Ta Kai Wa Masallaci A Garin Al-Fasha September 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsaron kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar
Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher
Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen.
Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in jin kai da ba a taba ganin irinsa ba. UNICEF ta bayyana cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan da aka yi bincike a kansu, a yayin da fada ke kara kamari da kuma kwararar ‘yan gudun hijira a Darfur.
A cikin rahotonta, UNICEF ta kara da cewa ta gudanar da bincike a wurare 88 tsakanin watan Janairu da Yuli na wannan shekarar, inda ta bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na Darfur, musamman a arewacin yankin, sun sami karuwar rashin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa na kashi 15 cikin 100.
Rahoton ya tabbatar da cewa adadin yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki ya karu zuwa sama da 315,000 a rabin farko na shekarar, karuwar kusan kashi 48 cikin 100 idan aka kwatanta da wannan lokacin a bara. Yayin da matsalar abinci ke ƙara ta’azzara, haka nan wahalar waɗanda suka ƙaura daga El Fasher zuwa Tawila a Arewacin Darfur ke ƙaruwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci