Zarif: Sake Kakaba Wa Iran Takunkumi Ba Zai Amfani Kasashen Turai Ba
Published: 27th, September 2025 GMT
Tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, har yanzu da akwai damar amfani da hanyoyin diplomasiyya domin warware batun Shirin Iran na makamashin Nukiliya da su ka hada da kafa wata cibiya ta tace uranium, da kuma sake sabunta hanyoyin aiki tare da hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa.
Tsohon ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da hanyoyin na diplomasiyya sun kunshi sake bude tattaunawa da kasashen turai uku, da kuma Rasha da China, kuma watakila Amurka ta shigo daga baya. Sai dai kuma minstan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa, sharadin samun nasarar ta fuskar diplomasiyya ya ta’allaka da idan kasashen turai sun daina halinsu na fuska biyu.
Muhammad Jawad Zarif ya kuma ce,bai san abinda kasashen turai suke son cimmawa ba,amma sakamanon da za su girba shi ne su fice daga zama abokan tattaunawa.
Bugu da kari, Muhammad Jawad Zarif ya ce, kasashen na turai sun yi wa Iran wasu alkawulla 11 da ba su yi aiki da ko da guda daya daga cikinsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD Ta Kara Yawan Kamfanonin Da Suke Taimakawa HKI A Laifukan Yaki Zuwa 68 September 27, 2025 Najeriya: Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wuraren Hako Zinariya September 27, 2025 Mahalarta Taron MDD Da Dama Sun Fice Daga Cikin Zauren Ayayin Jawabin Benjamine Netanyahu September 27, 2025 Wakilan kasashe sun fice daga zauren MDD, gabanin jawabin Netanyahu September 26, 2025 Larijani: Iran za ta katse hadin gwiwa da IAEA idan aka dawo mata da takunkuman MDD September 26, 2025 Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyar $ biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya September 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya Jaddada Cewa: Mallakar Makamashin Nukiliya Hakkin Iran September 26, 2025 Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya September 26, 2025 Kasashen Rasha Da China Sun Bukaci A Jinkirta Batun Maido Da Takunkumi Kan Kasar Iran September 26, 2025 Magajin Garin Landan Ya Yi Dirar Mikiya Kan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump September 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen turai
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa.
Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman a matakin yanki, kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da Majalisar Dinkin Duniya, wajen matsin lamba ga yahudawan sahayoniyya da magoya bayansu da su dakatar da kisan kiyashi da kuma janyewar ‘yan mamaya daga Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi juyayin tunawa da manyan shahidan gwagwarmaya, inda ta jaddada nauyin da ke wuyan kasashen duniya na hana duk wani cin zarafi daga ‘yan mamaya, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan da yaudara da karya alkawari da sahayoniyya suke yi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci