Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
Published: 16th, September 2025 GMT
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su.
Saboda haka, shawarar inganta jagorancin duniya ta zama wani abun dake biyan bukatun dake akwai a duniyarmu. Wannan ya sa ta samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.
Ta wannan shawara ta inganta jagorancin duniya, za mu iya kara fahimtar halayyar kasar ta Sin. Ko da yake wani yanayin da duniyarmu ke ciki shi ne dishewar tauraron kasashen yamma, amma duk da haka, kasar Sin ba ta neman yin koyi da kasashen yamma wajen yin babakere a duniya. Tana neman gyara, da inganta tsare-tsaren kula da harkokin duniya, ta yadda za ta tabbatar da moriyar dukkan kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, maimakon kafa wani sabon tsari da ya saba wa tsarin kasa da kasa na yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar diflomasiyya, shi ne kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama, da kokarin tabbatar da ci gaban harkokinsu na bai daya.
Yayin da karin kasashe ke nuna goyon bayansu ga shawarar kula da al’amuran duniya da kasar Sin ta gabatar, tabbas za mu shaida hadin gwiwar karin mutane a duniya don neman wanzar da adalci, abin da zai haifar da damar tabbatar da daidaito da adalci a duniyarmu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasashe masu tasowa a duniyarmu tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya
Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kafin al’ummar kasar Sin su cimma nasarar yaki da su.
A ranar 19 ga watan Agusta, hukumar kula da tsaron kasar Rasha ta fitar da wata takardar sirri da yanzu gwamnati ta mayar da ita ba ta sirri ba, wadda ta nuna cewa, domin neman yin amfani da makaman da aka hada da cututtuka a yakin kutsen da suka kaddamar a kasar Sin, reshen rundunar sojojin Japan da suka yi kutse a kasar Sin mai lambar 731, sun yi ta gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’umma, har ma sun kai harin boma-bomai da aka samar da cututtuka a kan daruruwan Sinawa, don neman tantance ingancin cututtuka ta hanyar kirga mutanen da suka harbu da cututtuka.(Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp