Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai
Published: 22nd, September 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan.
Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja.
Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa tushe da aka ƙirƙira da manufa ta yaudara.
A cewarsa, “kwanan nan, an yi wa jawabin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar ya gabatar a taron majalisun dokoki na Afirka (West African Parliamentary Conference, WAPC) mummunar fassara, har aka rika yi wa majalisar kuskuren fahimta cewar ba ta goyon bayan tsare-tsare da dabarun rancen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Wannan kuskuren fahimta ne, kuma ba gaskiya ba ce.”
Abbas ya jaddada cewa Majalisar Dokokin Tarayya baki ɗaya, sun amince cewa rance mai tsari cike da kulawa hanya ce da ake amfani da ita wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ƙarfafa ci gaban tattalin arziki, da kuma tallafa wa marasa galihu.
Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin jagorancin Tinubu, ana karkatar da kuɗaɗen rancen ne zuwa manyan ayyuka da suka haɗa da wutar lantarki, sufuri da noma, waɗanda za su ƙara inganta hanyoyin tattara kuɗaɗen shiga.
Abbas ya kuma tabbatar da cewa duk wani bashi za a karɓo shi ne cikin hikima da kuma tsare-tsaren rance na ƙasar na matsakaicin lokaci da wanda sun dace da duk wasu ƙa’idoji a fadin duniya.
Kazalika, ya jaddada muhimmancin kafa Ofishin Kasafin Kuɗi da Bincike na Majalisa (NABRO) domin yin bincike mai zaman kansa kan batutuwan rance, karɓo bashi da kuma manufofin kuɗi.
Sai dai shugaban majalisar ya yi gargaɗin cewa duk da yake karɓo rancen wajibi ne, amma buƙatar rufe ɓarakar sata da fitar da kuɗaɗen haramun ita ma babban lamari ne da ya zama tilas.
Ya bayyana cewa Najeriya na asarar kusan dala biliyan 18 duk shekara ta hanyar cin hanci da zamba da kuma halasta kuɗaɗen haramun — adadin da ya kai kusan kashi 3.8% na GDP.
Abbas ya ce haɗa rance mai tsari da kuma tsauraran matakan sa ido da yaƙi da cin hanci shi ne zai tabbatar da makomar tattalin arzikin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya rance tsare tsare
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale.
Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawaRahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar.
“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar da yaro ɗan shekara biyu, Danjuma Salman, wanda ya faɗa cikin wata rijiya da murfinta ya lalace,” in ji sanarwar.
Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun fito da yaron, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
An miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, Salman Dayyabu, bayan an fito da shi daga rijiyar.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Sani Anas, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen yaron.
Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da su riƙa rufe rijiyoyi da sauran wuraren ruwa yadda ya kamata domin guje wa irin wannan iftila’i.
Haka kuma ya shawarci iyaye da su riƙa kula da yaransu sosai, musamman a wuraren da ke da hatsari.