Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Shugaban Kasar Faransa
Published: 20th, September 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya mayar da martani kan zargin shugaban Faransa Emmanuel Macron
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya musanta zargin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a baya-bayan nan, yana mai jaddada cewa, a yayin da ministan harkokin wajen Iran ke magana, ko tattaunawa, ko ya aika da sako, ko gabatar da wata shawara, wannan mataki ya nuna ra’ayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana samun matsaya na cikin gida, kamar yadda aka gani a tattaunawar fahimtar juna tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a birnin Alkahira.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Gharibabadi ya yi ishara da shawarwarin baya-bayan nan da aka yi tsakanin Iran da kasashen Turai a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, yana mai cewa: A baya-bayan nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da shawarwari masu ma’ana da daidaito da nufin magance matsalolin da suke a matsayin damuwa.
Ya kara da cewa: “Wadannan shawarwari, kamar yadda Mista Macron da kansa ya nuna, sun kasance masu ma’ana kuma sun bude hanyar mu’amala da diflomasiyya. A saboda haka Macron ba zai iya kore su ba ko kuma ya yi la’akari da su a matsayin marassa wani muhimmanci, sai dai ya yi amfani da kalmar hankali wajen bayyana su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Faransa Zai Amince Da Kasar Falasdinu A Ranar Litinin Mai Zuwa A Birnin New York September 20, 2025 Tinubu Zai Dauki Nauyin Gasar Wasanni Commonwealth A 2030 September 19, 2025 Kungiyar Tarayyar Turai EU Ta Mika Bukatunta Ga Kasar Iran. September 19, 2025 Dakarun Sojin Yamen Su Kai Hare-hare A Muhimman Wurare A HKI. September 19, 2025 Isra’ila Na ci Gaba Da Kutsa Kai A Tsakiyar Gaza A Yau Juma’a September 19, 2025 Dangantaka Na Kara Tsami Tsakani Faransa Da Isra’ila Kan Falasdinu . September 19, 2025 Sojojin HKI 12 Ne Suka Halaka Ko Suka Ji Rauni A Gaza September 19, 2025 Amurka Ta Yi Amfani Da Kujeran Veto Don Hana Zaman Lafiya A Gaza September 19, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare Kan Wurare Har 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 19, 2025 Majiyoyin Diblomasiyya Sun Ce Washington Zata Jagoranci Turawa A Tattaunawa Da Iran September 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Husi: Kai Wa Kasar Katar Hari Gargadi Ne Ga Al’ummar Musulmi
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis ya bayyana cewa: Makaman gwagwarmaya suna a matsayin lamuni ne nah ana abokan gaba yi wa al’umma kisan kiyashi da hare-haren wuce gona da iri.
Da yake Magana akan abinda yake faruwa akan doron ruwan “Red Sea” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce; Duk wani yunkuri na bayar da kariya ga jiragen ruwan HKI, da kuma a cikin mashigan ruwa da suke a yankin, ba za su ci nasara ba.”
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Dukkanin hare-haren da su ka kai a makon da ya shude a ruwan “Red Sea” an kai shi ne akan jragen ruwan HKI kadai.
Har ila yau, ya kuma yi ishara da kisan kiyashin da HKI take ci gaba da yi wa al’umma Falasdinu a yankin Gaza, wanda lamari ne mai firgitarwa, kuma hakan ya tilasta wa duk wani ma’abocin lamiri a durin kasa daukar mataki.
Bugu da kari, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce, barazanar abokin gaba, ba ta tsaya akan Falasdinawa kadai ba, ya nufin dukkanin al’umma ne kadai,don haka bai kamata musulmi su yi sako-sako ba, ko su ci gaba da zama ‘yan kallon kisan da ake yi Falasdinawa.
Da ya koma Magana akan taron da aka yi a Doha ya bayyana cewa, jawabin bayan taro da aka yi, bai kai girman laifin da ‘yan sahayoniyar su ka tafka ba. Haka nan kuma ya ce; Matakin mai rauni na taron Doha, zai karfafa ‘yan sahayoniya su ci gaba da wuce gona da iri.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya bayyana Yadda Hadin Gwiwa Tsakanin Iran Da Rasha Ya Kawo Ci Gaba Tsakaninsu September 18, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Iran Ta Sauke Hakkin Da Ya Hau Kanta Sauran Bangaren Turai September 18, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Masu Goyon Bayan Isra’ila Suna Da Hannu A Laifukanta September 18, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Cika Kwanaki 713 Suna Kisan Kiyashi A Zirin Gaza September 18, 2025 Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa September 18, 2025 Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai September 18, 2025 Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci