Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya
Published: 17th, March 2025 GMT
A ranar Larabar da ta gabata ne, harajin kashi 25 na shugaban Amurka Donald Trump kan duk wasu kayayyakin karafa da goron ruwa ya fara aiki. Inda Kanada ta mayar da martani kai tsaye da harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka na sama da dala biliyan 20, wadanda suka hada da karafa, kwamfutoci da kayan wasanni.
EU ita ma mayar da martani da haraji kan kayayyakin Amurka na kusan dala biliyan 28, wanda zai fara aiki a ranar 13 ga Afrilu.
Hasashen dake tattare da manufar Trump shi ne, idan farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje ya tashi a dalilin karin haraji, to za a maida hankali kan kafa masana’antun cikin gida dake samar da irin wadannan kayayyaki, ta hakan za a samu karin ayyukan yi a Amurka. Sai dai Trump ya manta cewa, tsarin karin harjin kwastam na iya zama takobi mai kaifi biyu idan aka yi amfani da shi ba bisa ka’ida ba, kuma zai iya raunata wanda ke rike da shi. Wannan takobin a hannun Trump, yana barazanar zama “makamin lalata huldar cinikayya tsakanin kasa da kasa,” yayin da hakan ke mummunan tasiri ga tattalin arzikin Amurka.
Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Habaka Kasuwanci Da Karfafa Hada-hadar Kayayyaki Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya SuSanin kowa ne cewa Amurka ba za ta iya farfado da tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta da suka dade da bacewa a cikin dare guda ba, zai dauki watanni ko ma shekaru kafin a sake fasalin tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta, duk da cewa masu sayayya na Amurka sun riga sun tsunduma cikin matsalar hauhawar farashin kayayyaki na yau da kullum, sakamakon matakin kara haraji na Trump.
Bisa ka’ida, Trump yana da shekaru hudu ya cimma manufarsa, amma a aikace, lokacin ya yi kadan da zai gamsar da masu sayayya na Amurka. Idan har wannan manufar ta ci gaba da kasancewa a cikin watanni masu zuwa, to tabbas jama’a za su janye goyon bayansu ga shugaban, hatta a tsakanin ‘yan jam’iyyar Republican Congress, wadanda ya dogara da su wajen aiwatar da sabbin dokoki. Idan har suna ganin damar saken zabarsu na cikin hadari a zaben tsakiyar wa’adi na badi saboda tsarin tsuke bakin aljihu da matakin kara kudin fito da ya aiwatar, za su iya yin watsi da goyon bayan da suke baiwa shirin shugaban kasar. Tuni dai ana samun karuwar damuwa daga ’yan kasuwa, musamman wadanda suka dogara da tsarin samar da kayayyaki na duniya wanda manufar kudin fito ta Trump ta kawo ma cikas. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar.
“Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun.
“Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da suka nema, ba a samu cikakken yarda ba. Dukkan wadannan abubuwan dole ne a yi la’akari da su. Kafin wannan, majalisaun tarayya ba su da hurumin amincewa da kirkirar wata sabuwar jiha.
“Kamar yadda ake ciki a halin yanzu, babu jihar da aka ba da shawara a kirkira. Ba za mu iya tabbatar da rahotanni na karshe ba ko zartar da hukunci kan jin ra’ayin jama’a da aka hada ba har sai an kammala sauraron jin ra’ayin jama’a gaba daya zuwa lokacin da muka dawo,” in ji shi.
Ya jaddada cewa ‘yan majalisar za su ba da muhimmanci ga sha’anin kasa sama da ra’ayoyinsu a yayin yanke shawarar kan batun yin garambawu a kundin tsarin mulkin kasar nan.
“Majalisar tarayya dai wuri ne na yin dokoki da kuma kula da aikin tsarawa ko gyara kundin tsarin mulki. Muna kira ga ’yan’uwanmu ‘yan majalisa su yi amfani da wannan dama da za ta dace ga kowa da kowa.
“Muna maraba da shawarwari daga dukkan ‘yan Nijeriya da suka hada da dattawa da kwararru da shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da kungiyoyin matasa da kungiyoyin mata da kungiyoyin farar hula, har ma da ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje.
“Za a bude taron sauraron jin ra’ayoyin jama’a ga kowa, kuma kundin na karshe kan gyara tsarin mulkin kasar nan zai bayyana batutuwan da ‘yan Nijeriya suka yanke hukunci a kai, ba ra’ayin wata kungiya kadai ba.
“Manufarmu ita ce, tabbatar da duk wasu canje-canje da za a yi a kundin tsarin mulki su kasance mafi kyawu ga bukatar Nijeriya da kuma mutanenta,” in ji Adaramodu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp