Al’ummar A sassan Duniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa
Published: 6th, July 2025 GMT
An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza
A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara.
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan kare dangi a Gaza. Sun daga tutocin Falasdinawa da tutocin nuna kyamar yaki, yayin da wasu ke dauke da jajayen fulawa da aka lullube da fararen fulawa, wanda ke nuna alamar girmamawa ga yaran Gaza da aka kashe.
A Faransa, masu zanga-zangar sun yi maci a kan titunan birnin Paris, suna neman kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi kan al’ummar Falasdinu.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da rashin mutunta dokokin kasa da kasa tare da yin kira ga kasashen yamma karkashin jagorancin Faransa da su kakaba wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila takunkumi mai tsanani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Hukunta Gwamnatin Mamayar Isra’ila Dangane Da Ta’addancinta Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Iran laifi ne na yaki da ya zama wajibi duniya ta yi mata hukunci a kai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi kira da a dorawa mahukuntan yahudawan sahayoniyya alhakin munanan laifukan da suka aikata a kan al’ummar Iran, musamman a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a birnin Tehran fadar mulkin kasar da sauran garuruwan kasar ta Iran.
A wani sakon da ya wallafa a dandalin X a yau Asabar, Baqa’i ya ce, “Harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a asibitoci da kurkukun Evin a ranar 24 ga Yunin wannan shekara ta 2025, wanda ya yi sanadin shahadar fararen hula da ma’aikata da kuma masu shigewa da yawansu ya kai mutane 79, yana cikin laifukan yaki da kuma keta dokar jin kai ta kasa da kasa.”
Ya yi nuni da cewa, harin ya afku ne a daidai lokacin da iyalan fursunonin ke taruwa domin ziyartar ‘yan uwansu, kuma sun makale a karkashin baraguzan ginin inda suka yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri na jirgin saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila.