Aminiya:
2025-07-06@16:18:09 GMT

Mutun 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano

Published: 6th, July 2025 GMT

Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle.

Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe

Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM.

FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa suka yi karo da babbar motar.

Bayan aukuwar hatsarin, motocin biyu sun kama da wuta, inda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.

Kwamandan FRSC na Kano, MB Bature, ya ce jami’ansu sun isa wajen cikin gaggawa bayan samun rahoto.

Sun kuma kira ma’aikatan kashe gobara na jihar da na tarayya domin kashe gobarar da kuma ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce: “Mutum 24 ne hatsarin ya rutsa da su. Abin takaici, 21 sun rasu, yayin da uku suka jikkata.”

Gawarwakin da suka ƙone an kai su ɗakin ajiye gawa na Asibitin Nassarawa da ke Kano, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawa a Asibitin Gwamnati da ke Garun Malam.

Bayan haka, jami’an FRSC tare da taimakon ’yan sanda sun ɗauke motocin da suka tare hanya domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a titin.

Kwamanda Bature, ya bayyana alhininsa kan wannan mummunan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.

Ya kuma yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi.

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin direbobi su guji karya doka; kamar bin hanya ba daidai ba da tuƙin ganganci, wanda hakan ke haddasa haɗura.

“Wannan lamari abin takaici ne wanda ke nuna muhimmancin bin ƙa’idojin hanya. Mafi yawan haɗura za a iya kauce musu idan direbobi za su kiyaye doka,” in ji Bature.

Ya kuma buƙaci direbobi, musamman na motocin haya, da su guji gudu fiye da ƙima da ganganci a hanya, wanda a cewarsa shi ne babban dalilin da ke haddasa haɗura da asarar rayuka.

Ga hotunan yadda hatsarin ya auku:

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin mota Zariya hatsarin ya

এছাড়াও পড়ুন:

2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC

Yakubu ya jaddada kokarin hukuma wajen yin adalci.

“Za mu duba dukkan bukatun cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin wadanda suka kawo su ba, lallai hukumar zabe ba za ta taba karya ka’idojinta ba.”

Shugaban INEC ya musanta zarginsu cewa hukumar kokarin hada kai da wasu domin saba ka’ida wajen yin ragisara, ya tunawa da irin wannan zargin da ba tare da hujja ba da aka yi a shekarar 2013.

Ya bayyana cewa hukumar ta amince da dukkan wasikun da aka karba illa guda shida, wadanda za a yi aiki a kai kafin karshen mako. Haka nan ya lura cewa dokoki da ka’idojin zabe ta 2022 kan jam’iyyun siyasa yana nan a shafin intanet na hukumar.

Yakubu ya kara da cewa za a fitar da cikakken jerin kungiyoyi 110, ciki har da sunayensu da yadda ake takaitawa da adireshi, da sunayen shugabanninsu da sakatarensu, nan ba da jumawa ba za a wallafa su a shafin intanet na INEC da kafofin sada zumunta don tabbatar da gaskiyar lamari ga jama’a.

Daya daga cikin kungiyoyin masu neman zama jam’iyyun siyasa, ADA ana zargin cewa ta samu goyon bayan ne da hadakar wasu shahararrun mutane masu tasiri a siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi.

Wata kungiyar kuma wanda ake tsammanin tana samun goyon baya daga magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ta gabatar da bukatar rajista karkashin suna mai kama da na LP, wanda ke nuna damuwa game da yiwuwar maimaitawar sunan LP.

INEC ta ce akwai kura-kurai mai yawan gaske a cikin wasu takardun da aka gabatar. Wasu daga cikin kungiyoyin sun yi amfani da suna iri daya, wanda hakan ya sab awa ka’idodin INEC.

Kazalika, INEC ta gano cewa akwai kungiyar da ta gabatar da bukatar yin rajistar guda biyu, kowanne tare da shugabanci da adireshi daban.

INEC ta bayyana cewa za ta tantance dukkan bukatun bisa ga tsarin doka da ka’idojin aikinta kafin ta yi rajista ko ta ki.

Bugu da kari, INEC ta ce akwai bukatar da aka shigar mata na neman yin rajista daban-daban har guda biyu a karkashin sunan ‘Obidient Peoples Party’.

A cewarta, wasu ana takaita sunayenu sun yi kama da na jam’iyyun da aka soke rajistarsu a baya, kuma an shigar da wasu takardu ba tare da sa sunayen shugabannin jam’iyyar ba, wanda haka ya saba wa ka’idojin INEC.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano
  • Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
  • Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal
  • Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano
  • 2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC
  • Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa
  • “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa”
  • Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar
  • Filato: Mahara sun cire hannun matashi a kan hanyar komawa gida daga jana’iza