Babban Mufti Na Masarautar Oman Ya Yi Kakkausar Suka Kan Masu Son Kulla Alaka Da H.K.Isra’ila
Published: 6th, July 2025 GMT
Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila
Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe.
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba, babu wanda a can yake son ci gaba da zama a wannan kasa bayan sun ga cewa hakan ba ya cikin maslahar rayuwa.”
Al-Khalili ya ce: “Ta yaya wadanda suke da tushe zasu kulla alaka da gwamnati da zata gushe da hukuma wacce zata gushe ko ba dade ko ba jima.?
Babban Mufti na masarautar Oman ya kara da cewa: “Idan kana son sanin girman bala’i da girman masifa, to ka yi tunanin yadda alakarka zata kasance da mai dabi’ar dabbobi mai kashe fararen hula daga yara da mata da kuma tsofaffi, ta yaya zai kare maka naka hakkokin? Ya karkare bayanin da cewa: “Mutum ya halaka a cikin kwanakinsa na jarrabawa…idan baya iya bambance tsakanin mai kyau da maras kyau.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kasim Yace Kare Kasa Baya Bukatar Izini Daga Wani
Sheikh Na’in Kasem shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar bata bukatar Izini don kare kasar Lebanon daga makiyanta. Yama fadar haka ne ga wanda suka cika kunnen duniya kan cewa dole ne kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sheikh Kasim yana fada a wani jawabin da ya gabatar a ranakun Ashoora na Imam Hussain (a) ta kafar Bidiyo. Ya kuma kara da cewa wadanda suke maganar kungiyar Hizbullah ta mika makamanta ga gwamnatinsa kasar, ya fiye masu sauki su fadawa yan mamaya su fice daga kasar Lebanon su kuma dakatar da hare-haren ta’addancin da suke kawo mata.
Ya kara jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da rike makamanta sannan bata bukatar izini daga wani don kare-kasar Lebanon daga makiyanta.
Malaman ya kara da cewa, wani mai hankali ne zai amince ya mika makamansa a dai dai lokacinda mikiyan kasar Lebanon suna ci gaba da kawo hare-hare kan kasar a ko wace rana. Maimakon su yi allawadai da mai shisgigi sai suka sa idanso a kan makaman hizbulla.
Yace idan wasu a kasar Lebanon sun zami mika kai ga HKI da Amurka to wannan zaminsa ne, amma mu ba masu mika kai ga makiyammu ne ba. Shi’arimmu shi ne {bama daukar kaskanci}.
Ya ce kun yi kuskure da kuka dogara da karfin wasu don takurawa masu gwagwarmaya. Masu gwagwarmaya basa jin tsoron makiya. Ya ce manufarmu ita ce yantar da kasa daga hannun makiya itace manufarmu.
Ya kammala da cewa makiyarmu it ace HKI, dole ne ta fice daga kasar Lebanon, kuma gwagwarmaya ita ce hanya tilo ta korar yan mamaya daga kasarmu. Idan kuma wani yana ganin akwai wata hanya korar makiya daga kasarmu a shirye muke mu shiga tataunawa da shi, ya gamsar damu a kan shirin nasa.