IAR da NAERLS Sun Shirya Taron Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Noma Dawa A Najeriya
Published: 21st, March 2025 GMT
Cibiyar Bincike Kan Harkar Noma (IAR) tare da hadin gwiwar Hukumar Yada Sakamakon Bincike da Wayar da Kan Manoma ta Kasa (NAERLS), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sun shirya taron kwana guda a Kaduna domin masu ruwa da tsaki kan aikin bunkasa noman dawa a Najeriya.
Taken taron shi ne: “Gabatarwa da Tattaunawa Kan Amfanin Sabbin Nau’ikan Dawa Masu Jure Sauyin Yanayi Domin Rage Talauci da Inganta Abinci a Najeriya.
Daga cikin manyan abokan aikin akwai Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Kungiyar Manoman Dawa da Masara ta Najeriya, da Tarayyar Turai (EU), da sauransu.
A jawabin sa, Mataimakin Daraktan NAERLS, Farfesa Muhammad Musa Jaliya, ya ce babban burin taron shi ne tabbatar da dorewar sabon tsarin nomar dawa a Najeriya.
“Ba ma so mu gudanar da aikin kawai ya ƙare ba tare da dorewa ba. Babban dalilin wannan taro shi ne samar da mafita don dorewar aikin. Manoma sun rungumi aikin, kuma sun samu sauyi ta fuskar iri na dawa masu inganci da fa’ida,” in ji shi.
A tattauna da Radio Nigeria Kaduna, Shugaban Kungiyar Manoman Dawa ta Kasa, Dr. Adamu Yusuf, ya jaddada muhimmancin Najeriya a matsayin jagora a noman dawa a duniya. Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a da kokari domin kasar ta ci gaba da rike matsayinta a matsayin kasa ta daya ko ta biyu wajen noman dawa a duniya.
Ita ma a nata jawabin, Farfesa Aisha AbdulKadir daga IAR, ABU Zaria, ta bayyana cewa sun samu nasarar gabatar da sabbin nau’ikan iri na dawa a Najeriya.
“Muna son ganin mutane sun rungumi wadannan nau’ikan iri, muna kuma neman jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki da manoma don mu kara samun ci gaba,” in ji ta.
Wakilin ECOWAS a taron, Farfesa Mamman Saleh, ya bayyana cewa ECOWAS ta kuduri aniyar inganta rayuwar al’ummomin yankin ta hanyar bunkasa tattalin arziki da ayyukan noma.
“ECOWAS ta kafa hukumar kula da harkokin noma da albarkatun kasa domin tallafa wa ayyukan noman dawa na musamman, da nufin samar da ayyukan yi ga matasa da inganta gina kasa, da kuma dawo da filayen noma da suka lalace,” in ji shi.
Masu halarta taron sun fito ne daga Jihar Kaduna da sassa daban-daban da ke da alaka da harkar noman dawa.
Cov/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar.
Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna.
Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON).
Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin aikin hajjin.
“Lafiya maniyata aikin hajjin tana da matuƙar muhimmanci, mun zaɓi ayarin ne bisa ƙwarewarsu, kuma muna da tabbacin za su bayar da ingantaccen kulawa ta lafiya a lokacin aikin hajjin,” In ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken gwajin lafiya ga dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajj, musamman don gano mata masu juna biyu.
“Babu sassauci ko kaɗan wajen barin mata masu juna biyu su tafi Hajj.” in ji Malam Salihu, yana mai jaddada cewa gudunmuwar da ayarin likitocin za su bada wajen tabbatar da wannan doka, na da muhimmanci don bin ƙa’idodin aikin Hajjin.
Ya ja hankalin ayarin likitocin su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da sadaukarwa, domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu aikin hajji mai sauƙi cikin koshin lafiya.
Adamu Yusuf