NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu
Published: 21st, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma.
Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da dasa wasu ba, da tasirinsa kan sauyin yanayi da kuma lafiyarmu.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: duniya lafiya sare itatuwa Sauyin Yanayi
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kukah Centre ta ce ta kuduri aniyar horar da jami’an tsaro a jihohin Sokoto, Kaduna da Benue.
Daraktan Cibiyar Kukah Reverend Father Atta Barkindo, wanda ya bayyana hakan ya ce an dauki matakin ne domin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar al’ummar kasar.
Reverend Father Atta Barkindo, ya jaddada cewa an shirya horon ne domin inganta tsaro a tsakanin al’umma a cikin dimbin kalubalen da jihohi da dama ke fama da su a fadin kasar nan.
Ya kuma bayyana bukatar kafa jami’an tsaro na Jihohi su samar da ingantattun tsare-tsare don tabbatar da samar da ayyuka masu inganci.
Shima da yake jawabi, jami’in kula da ayyukan cibiyar Kukah, Terseer Bamber, ya yi nuni da cewa, wasu daga cikin jami’an tsaron jihar sun fuskanci tuhume-tuhume na take hakkin dan Adam da cin zarafin mata.
Ya jaddada mahimmancin magance wadannan matsalolin a matsayin wani abin da ake bukata domin samun ci gaba mai dorewa a Najeriya.
Ana aiwatar da aikin horon ne tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kukah, Ci gaban Ƙasashen Duniya na Birtaniya, da Tetra Tech International Development.
A nasa jawabin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar wanda Sarkin Yakin Gagi, Hakimin Gagi Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yi maraba da shirin inda ya bayyana cewa Sarkin Musulmi a shirye yake ya tallafa wa duk wani kokari da zai taimaka kai tsaye wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
Ya bukaci gwamnatocin jihohi da su ba da fifiko wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai, yana mai korafin cewa kalubalen tsaro ya yi matukar tasiri ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Rediyon Najeriya ya rawaito cewa taron ya samu halartar wakilai daga jami’an ‘yan sanda, da Civil Defence, masu aikin shari’a, ‘yan majalisar dokoki, da kuma shugabannin gargajiya, inda ya bayyana tsarin hadin gwiwa na inganta tsaro a Najeriya.
Nasir Malali/Sakkwato