Yemen Ta Ce A Shirye Take Ta Koma Yaki Idan Yaki Ya Sake Barkewa A Gaza
Published: 1st, March 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025.
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru.
Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu.
Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya a ayyukan tsagaita wutar, kuma ta na kallon yadda HKI take sabawa wasu abubuwan da ke cikin yarjeniyar. Ya kuma ambaci yadda HKI ta ki janyewa daga rafah da kuma yankin philidelfiya na kan iyaka da kasar Masar. Wanda kuma ya sabawa yarjeniyar. Sannan ya kammala da cewa gwamnatin kasar Amurka ta na kodaitar da HKI da yin hakan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.