Aminiya:
2025-05-01@02:23:07 GMT

Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya

Published: 17th, March 2025 GMT

Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa.

Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote.

NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi

Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, Shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne ga ‘yan Nijeriya a ƙananan hukumomi 774 na faɗin kasar nan, kamar yadda yake a tsarin kamfani da kuma gidauniyarsa na nuna jin-kai ga al’umma ƙasar nan.

Dangote, wanda ya samu wakilcin yarsa, Hajiya Mariya Aliko Dangote, ya ce: shirin na wannan shekara, an yi shi ne da nufin nuna tausayi da jinkai da nuna kulawa wajen taimakon jama’a bisa la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa da durkushewar tattalin arziki.

Ya ce gidauniyar ta fara kaddamar da rabon tallafin ne a Jihar Kano, sannan nan gaba za a ci gaba da rabawa sauran jihohi, domin tabbatar da ganin cewa abincin ya isa hannun wadanda aka yi domin su a daukacin kananan hukumomin kasar nan.

Alhaji Dangote, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar da Alhaji Aliko Dangote yake yi,wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilo 10 a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin Jihar Kano.

Da take jawabi ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Youssoufou ta ce an tsara shirin ne a matsayin wata hanya ta tallafa wa gwamnatoci wajen yaƙi da talauci da yunwa a Nijeriya.

Mukaddashin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Dokta Mujahid Aminudden ya gode wa gidauniyar ta Dangote kan bijiro da wannan shiri, inda ya roki sauran ‘yan Nijeriya da suyi koyi da halin Dangote.

Ya ce Hukumar Hisbah za ta tsaya tsayin daka wajen ganin tallafin yaje hannun waɗanda suka cancanta.

Wani da ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Malam Ibrahim Ahmed ya yaba wa Alhaji Aliko Dangote, inda ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da taimakonsa a harkokinsa na kasuwanci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gidauniyar Dangote Jihar Kano gidauniyar Aliko Dangote yan Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Kano: Galadima biyu a masarauta ɗaya

Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya.

A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa  matsayin sabon Galadiman Kano.

Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano.

Wannan sabon lamari ya biyo bayan rasuwar tsohon mai riƙe da muƙamin, Alhaji Abbas Sanusi —baffan Sarki Sanusi II kuma mahaifin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas.

Da farko, rikicin ya ta’allaka ne kawai kan wane ne halattaccen Sarkin Kano, tsakanin Sanusi da Aminu baya. Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Sarki na 15 Aminu Bayero, bayan soke dokar masarautun Kano ta shekarar 2019, wadda magabacin gwamnan kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya hannu a kai.

Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya

 

Bayan sauke shi, an mayar da Muhammadu Sanusi II — Sarki na 14 wanda a baya Ganduje ya tsige — a matsayin Sarki na 16 na Masarautar Kano, ɗaya ce daga cikin manyan masarautu mafiya ƙarfi da tasiri a Najeriya.

Sai dai, ’yan kwanaki bayan sauke shi, Aminu Bayero ya koma Kano ya zauna a ɗaya daga cikin ƙananan fadoji a unguwar Nassarawa, wanda ke daf da Gidan Gwamnatin Kano.

Tun daga wannan lokacin, kowanne daga cikin sarakunan biyu ke ta iƙirarin cewa shi ne halastaccen Sarkin Kano.

Sarki Sanusi II, wanda gwamnan Jihar Kano ya naɗa kuma gwamnatin jihar ta amince da shi a hukumance, a halin yanzu yana zaune a babban fadar sarki, Gidan Rumfa.

A daya hannun kuma ana ganin kusan dukkanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar, da kuma Gwamnatin Tarayya ma, suna sun amince da Sarki Aminu Ado Bayero.

Kowanne daga cikin sarakunan biyu na da majalisunsu a gidajensu daban-daban kuma suna ci gaba da halartar tarukan jama’a a ciki da wajen Kano.

A bisa doka, gwamnatin jiha kaɗai ke da ikon yin doka a kan al’amuran masarauta. Wannan yana nufin cewa, a bisa doka, gwamnatin jiha kadai za ta iya tantance wanda zai zama sarki da kuma naɗa masu riƙe da muƙaman sarauta.

Tarihin muƙamin Galadima a Masarautar Kano

Mukamin Galadima shi ne matsayi mafi girma da wani ɗan sarki zai iya samu a Masarautar Kano. A matsayinsa na babban mai riƙe da mukami a fada, ikon mallakar wanda zai riƙe muƙamin yana da matukar muhimmanci—don haka ne ma ɓangarorin biyu masu rigima da juna suke ƙoƙarin tabbatar da ikonsu a kai.

A tarihi, har ma Sarkin Kano na farko daga daular Fulani bayan Jihadin Usman Ɗanfodio a farkon shekarun 1800, Ibrahim Dabo, ya taɓa rike mukamin Galadima kafin ya hau karagar mulki. Babban ɗansa, Usman I, shi ma ya riƙe wannan muƙami mai daraja.

Hakazalika, Sarkin Kano na huɗu na Fulani, Abdullahi Majekarofi, ya kasance Galadima kafin ya zama Sarki. Babban ɗansa, Yusuf Maje-Garko, shi ma ya riƙe mukamin.

Bisa ga wannan al’ada, Sarki Bello, wanda ya gaje Majekarofi a matsayin Sarkin Kano, ya naɗa dansa a matsayin Galadima.

A tarihin baya-bayan nan, Muhammadu Inuwa, wanda ya zama Sarki bayan sauke Sanusi I a shekarar 1962, shi ma ya taɓa zama Galadima kafin ya hau karagar mulki.

Su wa aka naɗa Galadiman Kano?

Mutum biyu da aka nada a  wannan muƙami mai daraja na Galadima su ne Munir Bayero da kuma Sanusi Bayero.

Munir Bayero, wanda Sarki Sanusi II ya naɗa, baffansa ne. Kafin karin girman nasa, ya shi ne Wamban Kano kuma Hakimin Bichi.

A lokacin da Sarki Sanusi ya kasance Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Munir Bayero ya yi aiki a matsayin daya daga cikin mataimakansa.

Daga baya da Sanusi II ya zama sarki, ya nada shi Hakimin Bichi —wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce sosai.

A wani lokaci, har ma Sarki Sanusi ya shirya zuwa tare da shi da kansa zuwa sabon masarautarsa, amma jami’an tsaro suka killace fadar Kano kuma suka hana tafiyar.

A ɗaya ɓangaren kuma, Sarki Aminu Ado Bayero ya naɗa Sanusi Bayero, babban dan marigayi Sarki Aminu Ado Bayero, kuma ɗaya daga cikin manyan ’yan takarar sarautar Kano bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 2014. A lokacin shi ke riƙe da sarautar Ciroman Kano, amma masu zaɓen sarki suka zabi Sanusi II a matsayin sarki.

Don nuna rashin amincewa, Sanusi Bayero ya ki yin mubaya’a ga sabon sarkin. A sakamakon haka, Sarki Sanusi II ya sauke shi daga mukaminsa, kuma Sanusi Bayero ya koma Abuja.

Bayan da Gwamna Ganduje ya sauke Sanusi II a shekarar 2020 kuma ya maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero, sabon sarkin ya dawo da Sanusi Bayero, inda ya naɗa shi a matsayin sabon Wamban Kano.

Amma a lokacin da aka dawo da Sanusi II a matsayin Sarki a shekarar 2024, bai amince da muƙamin Sanusi Bayero ba.

 

‘Karin naɗe-naɗe masu karo da juna na nan tafe’

Bayan muƙamin Galadima, Sarki Sanusi II ya kuma sanar da naɗa wasu sabbin masu muƙamai guda hudu, tare da ƙarin girma ga wasu biyu.

Sabbin wadanda aka naɗa sun hada da Kabiru Hashim a matsayin Wamban Kano, Mahmud Ado Bayero a matsayin Turakin Kano, Ado Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano, da Ahmed Abbas Sanusi a matsayin sabon Yariman Kano.

A halin da ake ciki kuma, majiyoyi daga fadar Nassarawa sun bayyana cewa Sarki Aminu Ado Bayero ya riga ya kammala shirye-shiryen mayar da martani ga waɗannan naɗe-naden da nasa jerin mutanen.

Siyasa ce tsantsa – Dr Kurawa

Da yake zantawa da Daily Trust kan yadda al’amura ke ƙara dagulewa, wani mai bincike, marubuci kuma masanin tarihi mazaunin Kano, Dakta Ibrahim Ado Kurawa, ya yi zargin cewa duk dambarwar sarautar Kano gwamnatin tarayya ce ke tunzura shi kuma take mara baya, saboda abin da ya bayyana a matsayin son zuciyarta a cikin lamarin.

Dakat Kurawa ya ce, halattacciyar iko na hannun gwamna, kuma sarkin da gwamna ya amince da shi ne kawai ke da ikon doka na nada masu muƙamai.

Ya ce, “Siyasa ce tsantsa, saboda Gwamnatin Tarayya ta nace cewa dole Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama Sarkin Kano duk da rashin ikon aiwatar da hakan. Da Gwamnatin Tarayya ba ta da wani muradi a ciki, ba zai yi wannan ba.

“Da farko, shi [Aminu] bai ma ƙalubalanci sauke shi a kotu ba da kansa. Yana kawai dogaro ne da ƙararrakin wasu mutane, yana fatan za a mayar da shi kan karagarsa.

“Kuma a al’ada, duk wanda yake cikin Gidan Rumfa shi ne halattaccen Sarki. Duk wani mutum kuma bogi ne kawai. Kafafen yada labarai ne kawai ke ci gaba da ingiza rikicin ta hanyar da’awar cewa akwai sarakuna biyu a Kano alhali a zahiri, shi (Aminu) ba shi da ko da hakimin unguwa.”

Kurawa ya ci gaba da bayanin cewa, “Duk hanyoyin mulki suna hannun gwamna, kuma ya riga ya miƙa su ga wani. Ba ku san cewa har a Jihar Sakkwato a yau, Sarkin Musulmi ba zai iya naɗa ko da hakimin unguwa ba sai da amincewar gwamna? Don haka me ya sa na Kano zai bambanta? Abu ne mai sauƙi—son zuciyar gwamnatin tarayya.

“Misali, tsohon Sarkin Gwandu, Mustafa Jokolo, ya ƙalubalanci sauke shi a kotu, amma shin ya kafa wata majalisar fada a Gwandu? A’a. Saboda Gwamnatin Tarayya ba ta da wani muradi a shari’arsa.

“Idan kana ƙalubalantar ikon gwamna kuma kana da goyon bayan wata babbar hukumar tarayya, wasan kwaikwayon zai ci gaba saboda kana da hanyoyin mulki da za ka iya ci gaba da shi,” in ji shi.

Daga Sani Ibrahim Paki & Ahmad Datti, Kano

Fassara; Sagir Kano Saleh

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta ƙaddamar Da Sabon Shafin Intanet Don Inganta Sayayya A Tsakanin Ma’aikatunta 
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Kano: Galadima biyu a masarauta ɗaya
  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
  • Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba 33 A Kano
  • Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
  • Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano