Ba Atiku kaɗai ba ne matsalar PDP — Gwamna Lawal
Published: 19th, June 2025 GMT
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar.
Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba ne; ta wuce hakan.
“Matsala ce daga cikin gida… Na ga matsalar tana da alaƙa da girman kai, ba a bar kowa a baya ba.”
Da aka tambaye shi ko yana daga cikin masu haddasa matsala a cikin jam’iyyar, ya amsa cewa yana ciki.
Gwamna Lawal, wanda shi ne gwamnan PDP na farko a Jihar Zamfara, ya ce yana da yaƙinin cewa har yanzu za a iya gudanar da zaɓe na gaskiya a Najeriya.
“E, har yanzu za a iya gudanar da zaɓe na gaskiya… Shi ya sa aka zaɓe ni a matsayin gwamnan Jihar Zamfara.”
PDP na fama da rikici tun bayan rashin nasararta a zaɓen 2023. Manyan ’yan jam’iyyar da dama sun sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da gwamnoni daga jihohin Akwa Ibom da Delta. Wannan ya rage ƙarfin jam’iyyar a wasu yankuna.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya fara tuntubar wasu manyan ’yan siyasa irin su Peter Obi da Nasir El-Rufai don kafa haɗaka kafin zaɓen 2027.
Ya ce yana yin haka ne domin guje wa Najeriya komawa jam’iyya ɗaya.
Amma wasu jagororin PDP ba sa goyon bayan wannan ƙawancen.
Jigo a jam’iyyar, Bode George, ya ce yana da kyakkyawan fata cewa PDP za ta iya warware rikicinta na cikin gida kafin taron jam’iyyar karo na 100.
INEC ta ƙi aminta da babban taron PDPA gefe guda kuma, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, (INEC), ta ƙi amincewa da gayyatar taronta saboda rashin cika sharuɗan da doka ta gindaya.
Gayyatar ta samu sa hannun mukaddashin shugaban jam’iyyar kaɗai, ba tare da na sakataren jam’iyyar ba, wanda doka ta buƙata.
Ana sa ran taron da aka tsara yi a ranar 30 ga watan Yuni, 2025 zai tattauna kan rikice-rikicen PDP na cikin gida, batun shugabanci, da kuma yadda za a ware tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027, inda wasu ’yan jam’iyyar, musamman G5, ke buƙatar a bai wa Kudu damar yin takara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Lawal Siyasa taro Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya.
El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya.
Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a TarabaYa ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Najeriya sun sauke APC daga kan mulki.
“Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya zai lalace.
“Ƙasar na iya fuskantar barazana,” in ji shi.
“Wannan dai ta zama gwagwarmaya don ceto rayuwarmu.”
El-Rufai, ya ce dawowarsa siyasa ba don wata riba ko matsayi ba ne, sai don yana ganin gwamnatin yanzu ta gaza.
“Ba don ƙashin kaina nake wannan ba. Na dawo siyasa ne domin na yi wa al’umma hidima. Idan gwamnati ba ta cika alƙawari ba, dole ne na fito na faɗi gaskiya kuma na ɗauki mataki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa haɗakar ADC an kafa ta ne domin yaƙar manufofin APC.
Ya ce gangamin da aka yi a Sakkwato shi ne farkon matakin neman goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar nan.
El-Rufai, wanda ya ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar a watan Maris, 2025.
Ya koma jam’iyyar SDP, saboda rashin jin daɗin yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya.