Kar a kuskura a shiga cikin yaƙin Iran da Isra’ila — MDD
Published: 19th, June 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar wuta a rana ta shida.
Ita ma ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci bangarorin biyu, da su kare fararen hula yayin da adadin mace-mace da jikkata ke ci gaba da karuwa.
Babbar sakatariyar ƙungiyar ta kasa da kasa, Agnes Callamard wadda ta yi wannan kira, ta buƙaci Iran da Isra’ila da su martaba haƙƙoƙin jama’a, tare da tabbatar da cewa ba fararen hula a ƙasashen biyu ne ake gasa wa tsakuwa a hannu sakamakon wannan rikici ba.
Rikicin dai ya fara ne a ranar Juma’a, lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da wani gagarumin harin bama-bamai wanda ya sanya Iran mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.
Tuni dai jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta amince da ƙarfa-ƙarfan zaman lafiya ba, yana mai gargaɗin Amurka cewa muddin ta kai musu hari, to za ta ɗanɗana kuɗarta.
Kalamansa na zuwa ne a yayin da Isra’ila ta ce ta kai hari kan wurare 40 a cikin Iran a wannan Larabar da suka haɗa da masana’antar ƙera makamai, yayin da ita ma Iran ta kadddamar da farmakin jirage marasa matuka kan Isra’ila.
A ɓangare guda, Rasha da Amurka na ganawa da juna da zummar lalubo zaren warware rikicin kamar yadda mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Ryabkov ya bayyana.
Tun da farko ya gargaɗin cewa, muddin Amurka ta shiga cikin yaƙin kai-tsaye domin taimaka wa Isra’ila, to babu shakka hakan zai sake jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin ruɗani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp