ECOWAS Za Ta Aika Kwamitin Sulhu Zuwa Kasashen AES
Published: 6th, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.
Ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka gudanar a Legas.
A cewar Sanata Barau, manufar kwamitin ita ce tattaunawa da shugabannin kasashen AES don fahimtar juna da jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewa cikin ECOWAS, musamman idan aka yi la’akari da dangantakar tattalin arziki da zamantakewa da ke tsakanin jama’ar yankin.
Shugabar Majalisar Dokokin ECOWAS, Hadja Memounatou Ibrahima, ta ce kafa kwamitin zai taimaka wajen shawo kan matsalolin siyasa a yankin da kuma hana ƙarin ƙasashen Yammacin Afirka ficewa daga ECOWAS.
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka hade a karkashin Kawancen Kasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS.
Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin kungiyar da kasashen AES, domin har yanzu ana ci gaba da hulda tsakanin al’ummomin yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Samu Babban Canji Kan Tsarin Ciniki A Tsakanin Sin Da Afirka
Bisa rahoton bunkasar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da nahiyar Afirka na shekarar 2025, wanda aka gabatar a jiya Juma’a 13 ga wata, an ce a halin yanzu, an samu babban sauyi a tsarin ciniki tsakanin Sin da Afirka, an kuma kyautata tsarin zuwa mai shafar fannoni da dama, mai inganci, mai kunshe da fasahohin zamani, kana a nan gaba za a samu karin damar hadin gwiwarsu a fannonin masana’antu, da aikin noma, da sadarwa, da tattalin arziki ta yanar gizo, da ayyukan more rayuwa, da makamashi mai tsafta, da hada-hadar kudi da sauransu.
A matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma a gun bikin baje koli na tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka karo na 4, an gabatar da rahoton ne a taron gabatar da shirye-shiryen ayyukan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka, wanda aka gudanar a wannan rana.
Rahoton ya yi bayanin cewa, a shekarun baya-baya nan, an fadada cinikayyar Sin da Afirka, yawan kudin cinikayyar kaya tsakaninsu a shekarar 2023 ya zarce dalar Amurka biliyan 280, kuma yawan kudin cinikin hidimomi a tsakaninsu a shekarar 2021 ya kai sama da dalar Amurka biliyan 41 da miliyan 866, kana an kyautata tsarin cinikinsu.
A daya bangaren kuma, yawan jarin da Sin ta zubawa Afirka ya karu, wanda yawancinsu suka shafi sha’anin gine-gine. Haka zalika, an samu nasarori a fannin gina ayyukan more rayuwa, da gudanar da ayyuka a fannonin sufuri, da wutar lantarki, da sadarwa, da madatsun ruwa da sauransu, da kuma yin hadin gwiwarsu a fannonin ba da ilmi, da aikin noma, da kiwon lafiya, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp