’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina
Published: 19th, June 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe akalla manoma 20 da wasu mutum uku da kuma wani dan sinitiri a jihar Katsina.
An kashe mutanen ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai karamar hukumar Kankara, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da kalubalen tsaro a jihar.
A cewar wani mazaunin yankin da bai amince a bayyana sunansa ba, “Kimanin kwanaki shida da suka gabata ’yan bindiga suka kai hari kauyukan Yargoje, Kwakware, Danmarke, Gidan Dawa da kuma Burdugau.
“Sun kashe kusan manoma 20, sun sace wasu sannan suka sace shanun da manoman ke amfani da su wajen huda a gonakin nasu,” in ji shi.
Kazalika, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa a ranar Litinin ’yan bindiga sun kai hari kauyen Marmara, shi ma da yake karamar hukumar ta Kankara, inda suka fafata da wasu masu aikin sintiri a yankin da ake kira da C’Watch da wasu ’yan sa-kai, inda suka kashe dan sintirin daya sannan suka jikkata masu aikin sa-kai biyu a kusa da kauyen.
“Sannan sun sami nasarar shiga kauyen Marmara, inda suka kashe mutum uku,” in ji majiyar.
Wakilinmu ya kuma gano cewa a dai daren Litinin din, maharan sun farmaki wasu kauyuka da ke kusa da Kwakware, inda suka sace mutanen da ba a san adadinsu ba.
Wani mazaunin yankin da shi ma bai amince a bayyana sunansa ba ya ce karuwar hare-hare a karamar hukumar a ’yan kwanakin nan ba zai rasa nasaba da yadda wasu kananan hukumomin da ke da makwabtaka da ita suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba.
“Saboda matukar za a samu yarjejeniyar zaman lafiya a wasu wuraren ba a ko ina ba, akwai yiwuwar su farmaki wuraren da ba su da yarjejeniyar zaman lafiyar,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025