Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda.

A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.

Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna da hanyoyin da ake ginawa da kuma tashar samar da wutar lantarki ta ruwa, watau tashar samar da wutar lantarki ta Nyabarongo kashi na II, wadda kasar Sin ke tallafawa a kan aikinta.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.

Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.

Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaidai Dake Kasar Yamen
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki