Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC
Published: 17th, June 2025 GMT
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin.
Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar nan ta garkuwar da mutane domin neman kuɗin fansa.
Ya bayyana cewa kaurin suna da ’yan yahoo suka yi a matsayin miyagu sun shafa wa kowane ɗan Nijeriya bakin fenti da duk inda suka shiga ake ɗari-ɗari da su a matsayin masu laifi.
Shugaban na EFCC ya ce a yanzu da zarar miyagun ’yan siyasa sun samu damar yin ruf da ciki a kan dukiyar kasa, sukan haɗa kai da waɗannan matasa ’yan yahoo-yahoo su boye kuɗaɗen a cikin wani asusun yanar gizo da ake kira wallet.
“Sau tari irin waɗannan ’yan siyasa sukan jibge ’yan yahoo a otel-otel su rika buɗe musu asusun ajiya na kirifto su boye biliyoyin kuɗaɗen da suka sata.”
Olukoyede ya buga misali da wani matashi mai shekaru 22 da hukumar ta kama yana yi wa ’yan siyasa irin wannan aika-aikar wanda aka gano ya samu tukwicin Naira biliyan biyar a tsawon watanni 18 kacal.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Yahoo Satar kudi
এছাড়াও পড়ুন:
Matashi ya rasa ransa a kan soyayya a Yobe
Wani matashi mai shekaru 20, Jibrin Saidu Lamido, ya rasa ransa bayan wani rikici a kan soyayya da ya auku ƙauyen Gurdadi da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je zance wajen budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri.
Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35 Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — GwamnatiWata majiya ta ce wani mutum da ba a san ko waye ba ya zo wajensu, tare da tafiya da budurwar sannan ya ƙalubalanci Jibrin da ya biyo su idan shi “namijin gaske ne.”
Daga nan ne rikici ya ɓarke tsakaninsu, inda wanda ake zargi ya daɓa wa Jibrin adda a wuya.
“An garzaya da shi zuwa asibitin Kumaganam amma likita ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji majiyar ’yan sanda.
Rundunar ’yan sandan jihar ta miƙa gawar mamacin ga iyayensa don yi masa jana’iza.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa suna ci gaba da neman wanda ake zargi, wanda ya tsere bayan aikata laifin.