NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na
Published: 19th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.
Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya. NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya Wahala DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cutar amosanin jini cutar sikila
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa babu ma’aikatan jinya da za su duba ta da sauran wadanda aka shirya za a duba su a ranar Alhamis. Da aka tambaye ta game da matakin da za ta dauka na gaba, Misis David ta ce za ta koma gida har sai an dakatar da yajin aikin. Mista Nde Danladi John daga karamar hukumar Kanke wanda shi ma ya zo ya kwashe iyalinsa, ya ce babu wanda ya duba su a asibiti tun ranar Laraba. Haka kuma, a sashen kula da lafiya na matakin farko na Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, ba a ga wata ma’aikaciyar jinya da ke kula da marasa lafiya ba yayin da likitan da ke bakin aiki ya halarci wasu tsirarun marasa lafiya, ya ce sauran su dawo ranar Juma’a. Wakilinmu ya ruwaito cewa, yajin aikin da aka fara da tsakar daren ranar 30 ga watan Yuli, 2025, ya janyo janyewar ma’aikatan jinya da ungozoma baki daya a dukkanin cibiyoyin lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp