Jami’an Tsaron Kan Iyakar Iran Sun Harbo Jiragen Masara Matuka 44 Na Sojojin H.K.Isra’ila
Published: 16th, June 2025 GMT
Jami’an tsaron kan iyakokin Iran sun harbo jiragen saman yaki marasa matuki ciki guda 44 a cikin sa’o’i 48 da suka gabata
Kwamandan rundunar tsaron kan iyakokin kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Ali Goudarzi ya bayyana cewa: An harbo jiragen sama marasa matuka ciki guda 44 da kananan jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya tare da lalata su a wasu kan iyakokin kasar.
Birgediya Janar Goudarzi ya bayyana a ranar Lahadi cewa: “Bayan harin da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kaddamar kan Iran, a cikin sa’o’i 48 da suka gabata, jami’an tsaron Iran sunsamu nasarar kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki na gwamnatin ‘yan sahayoniyya guda 44 da kananan jiragen sama na wannan muguwar gwamnati, sakamakon Sanya ido kan shige da ficen kan iyaka ta sararin samaniyya.”
Haka nan kuma yayin da yake ishara da cikakken shirin da dakarun tsaron kan iyakokin kasar suka yi na sa ido da kuma kiyaye iyakokin kasar Iran, ya kara da cewa: Jajirtattun jami’an tsaron kan iyakokin kasar Iran, tare da cikakken shirinsu na kula da tsaron kan iyakokin, sun gargadi dukkan makiya, ‘yan ta’adda, kungiyoyin masu dauke da makamai, da masu fasa kwauri da cewa za su mayar da martani da karfi kan duk wani hari da aka kai kan tsaron kan iyakokin kasar.
Birgediya Janar Goudarzi ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga sauran sojojin kasar, inda ya jaddada sanya ido kan bayanan sirri don tabbatar da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma tunkarar duk wata barazana a kan iyakar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsaron kan iyakokin kasar an tsaron kan
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA