HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe
Published: 18th, June 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara asibiti da ke Makurdi, Babban Birnin Jihar Benuwe, domin duba waɗanda da suka jikkata a hare-haren da ‘yan bindiga suka jihar.
Shugaban ya je ne domin ganin irin ɓarnar da aka yi, tare da nuna alhini da goyonnsa baya ga al’ummar jihar.
Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin SakkwatoHotunan ziyayar sun nuna Tinubu yana duba da waɗanda abin ya shafa.
Go hotunan a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata.
Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya ji ciwo mai tsanani a wajen. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Panorama inda aka ɗinke masa raunin da ƙwayoyin da suka kai guda shida.
Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa BarcelonaƘungiyar ƙwallon ƙafa ta Aris FC, wacce ta karɓi Perez aro daga Celta Vigo, ta tabbatar da cewa ya samu “cizon da ya haddasa kumburin naman wajen,” kuma hakan ya sa ba zai buga wasan UEFA Conference League da za su kara da Araz-Nakhchivan ranar Alhamis ba.
Kocin ƙungiyar, Marinos Ouzounidis, ya bayyana cewa an tsara Perez zai fara wasan kafin lamarin ya faru. “Carles zai kasance cikin ƴan wasa 11 na farko da zasu fara fafatawa” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp