An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano
Published: 19th, June 2025 GMT
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su.
Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi.
’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a ZamfaraA kotun, an gurfanar da su kan laifukan haɗa baki domin tayar da hankali, jikkata mutum, hana ‘yan sanda yin aikinsu yadda ya dace, da kuma ɓoye wanda ake zargi.
Lauyan gwamnati, Barrista Aliya Ibrahim Aminu ce, ta karanta musu tuhumar a gaban kotu.
Ɗaya daga cikinsu ya musanta laifin, yayin da Idris Ado da wasu mutum biyar suka amsa wasu daga cikin tuhumar amma suka ƙi amincewa da sauran.
Alƙalin kotun, Khadi Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini, ya yanke musu hukuncin ɗaurin wata uku bisa laifin farko, da wata uku a laifi na biyu.
Haka kuma ya ƙara yanke musu hukuncin ɗaurin wata uku tare da tarar Naira 15,000.
Za a yi wa kowannensu bulala 20.
Baya ga haka kuma, kotun ta umarce su da su yi wata shida a ƙarƙashin kulawa, inda za su riƙa share magudanan ruwa a unguwanninsu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp