Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti
Published: 18th, June 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan.
Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa.
Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, AlbarnawiA yayin ziyarar tasa ta yini guda, Shugaba Tinubu ya fara ne da ziyartar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwe, inda ta duba waɗanda suka jikkata.
Shugaban ya shirya ganawa da iyalan waɗanda aka kashe, da waɗanda suka rasa muhallansu, da kuma shugabannin al’umma.
Hakazalika, Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki s jihar, ciki har da sarakunan gargajiya, ’yan siyasa, shugabannin addinai, da ƙungiyoyin matasa.
Burinsa shi ne samo hanyar kawo ƙarshen rikicin da ya addabi yankunan Yelwata, Apa, da kuma Agatu.
Yadda rikicin ya samo asaliRikicin a Jihar Benuwe ya daɗe ana tafka shi, kuma mafi yawan lokuta rikici ne tsakanin manoma da makiyaya.
Manoma na zargin cewa shanun makiyaya na lalata gonakinsu, yayin da makiyaya ke kukan rashin wuraren kiwo.
A watan Afrilun shekarar 2023, sama da mutum 50 ne suka rasa rayukansu a ƙauyen Umogidi da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo.
A watan Yunin 2023 kuma, an kai farmaki ƙauyuka da dama a Guma da Logo, inda mutane da dama suka mutu.
An daɗe ana zargin wasu daga cikin hare-haren ƙungiyar Miyetti Allah da wasu ’yan bindiga ne ke kai wa.
Yawancin mutane sun rasa gidajensu da gonakinsu, wasu kuma sun tsere zuwa sansanonin ’yan gudun hijira.
Duk da irin ƙoƙarin da gwamnonin da suka gabata suka yi, har yanzu matsalar na ci gaba da faruwa.
Ziyarar Shugaba Tinubu tana ƙarfafa wa mutane gwiwa cewa za a iya samo mafita domin kawo ƙarshen kashe-kashen da ke faruwa a Benuwe da sauran wuraren da rikicin ya shafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hare hare tattaunawa Zaman lafiya ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a KolmaniA cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.
Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.