Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF.

An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da suka raba kudaden Anchors Borrowers, guda 9 ne kawai, ‘yan majalisar ke da masaniya kansu. Okafor ya ce, daya daga cikin muhimman ayyukan kwamitin shi ne, tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen tallafi da hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka yi a fannin samar da abinci da tattalinsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano.

Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman.

Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono

Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar.

“Mun fara wannan shiri fiye da shekara guda da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai. Yanzu mun zo nan don fara na ɓangaren jarirai. Mu za mu biya kudin kulawar gaggawar yaran sannan mu tabbatar an kula da su har su samu ingantacciyar lafiya,” in ji Dr. Sikiru.

Ya kuma ce a karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi, amosanin jini, cutar shawara da yaran da aka haifa bakwaini da ma cututtukan da ke buƙatar tiyata za su samu kulawa kyauta.

Ya ce asibitoci za su fara ba da kulawa da zarar an kawo yara, sannan su tura adadin kuɗin kula da yaran a kowanne mako ga NHIA don a biya su.

Daraktan ya kara da cewa duk yaran da ya sami kulawar gaggawar kuma, za a saka shi cikin shirin inshorar lafiya na NHIS, inda hukumar za ta ci gaba da biyan kudin inshorar don tabbatar da samun kulawar lafiya mai inganci.

“Kafin yaro ya ci gajiyar shirin, dole ne a tantance shi a a tabbatar yana da rauni da kuma ba zai iya biyan kuɗin asibiti ba. Haka nan dole ne yaro ya mallaki Lambar Shaida ta Kasa (NIN) don tabbatar da gaskiya da shigar da su cikin tsarin,” in ji shi.

Dr. Sikiru ya kuma ce, “Shiri ne kula da marasa lafiya cikin gaggawan. Da zarar sun zo, za a duba su. Asibitin sai ya turo mana jimillar adadin kudin, mu kuma mu biya.”

Ya ce wannan shiri wani bangare ne na kudurin gwamnatin tarayya na rage mace-macen jarirai da tabbatar da cewa babu yaron da ya rasa kulawar asibiti saboda rashin kudi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa