A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya.

 

Tsohon shugaban ƙasar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba, mai ci gaba kuma sabuwar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin ka.

 

“Ga mu nan. Abubuwa biyu sun ba ni mamaki: Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa kun samar da na’urorin CT scan da MRI Machine, na san wasu asibitocin koyarwa ba su da CT scan da MRI, wasu kuma suna da shi amma ba sa aiki. Ku ga na ku, yana aiki ga al’umma.

 

“Na yi matuƙar farin cikin kasancewa a nan, don ƙaddamar da wannan asibitin da aka gyara da kuma saka kayan aiki na zamani don jin daɗin duk wanda zai zo nan.”

 

Da yake ƙaddamar da titin Zannah zuwa Abarma, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya bayyana cewa, Gwamna Lawal na mayar da Zamfara jiha ta zamani.

 

“A bisa abubuwan da na gani da idanu na da kuma wanda na ji, mu abokan haɗin gwiwa ne a ci gaba. Ina roƙon ka da ka ci gaba da inganta jihar Zamfara a tsawon shekaru takwas da gwamnatin ka za ta yi.”

 

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya gode wa tsohon shugaban ƙasa Obasanjo bisa amsa gayyatar da aka yi masa na ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar.

 

“Ranka ya daɗe, a madadin ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara, muna godiya da karrama mu ga amsa gayyatar da muka yi maka, da kuma maraba da zuwa gidanka na biyu, Jihar Zamfara, Jihar da ka ke kyauna a zuciyarka, domin sana’armu ta farko a nan ita ce noma, kuma wani abu ne da ka ke sha’awa.

 

“Asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura ya bi tsarin faɗaɗawa da ingantawa, an kuma gina sabbin gine-gine, a yanzu haka likitocin suna da sabbin gidajen zama da aka kammala, waɗanda suka haɗa da rukunin gida mai ɗakuna biyu da mai uku, da kuma wurin zama da ya dace da Babban Daraktan Lafiya.

 

“An kuma samar da filin da mara lafiya zai shaƙatawa cikin natsuwa tare da ƙawata yanayin asibitin. Mun kuma inganta hanyoyin cikin asibitin don sauƙaƙa zirga-zirga da ƙayatar da harabar asibitin.

 

“Sabbin cibiyoyin da aka gina su ne Sashin Kula da Mata (O&G), sabon rukunin Radiology, sashin ɗakin gwaje-gwaje, da filin shaƙatawa na marasa lafiya.

 

“Ginshiƙi shi ne gyara muhimman sassa guda 14, waɗanda dukkansu an sake farfaɗo da su tare da inganta su zuwa matsayin zamani.

 

“Mun saka duk waɗannan kayayyaki na zamani a wuraren da suka dace kuma masu muhimmanci. Waɗannan sun haɗa da saka na’urori na zamani a bangaren don radiology, wankin ƙoda, tiyata, ophthalmology, ENT, physiotherapy, endoscopy, echocardiography, haƙori, da kuma kula da lafiya gaba ɗaya.

 

“An kuma ba wa asibitin sabbin gadaje na majiyyata, na’urorin lantarki, kayan ɗaki, da kayayyakin tattara shara don tabbatar da tsaftar muhalli da bin ƙa’idojin tsabta na duniya.”

 

Gwamnan ya jaddada cewa asibitin yana da ingantattun kayan aiki don aiki a matsayin cibiyar tuntuɓar likitoci, ingantaccen wurin horar da ma’aikatan kiwon lafiya kuma cibiyar bincike da ƙididdiga ta likitanci.

 

Sauran ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da titin Zannah zuwa Abarma da titin Tsalha Bungudu zuwa Kwanar Birnin Ruwa, duk a Gusau babban birnin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jihar Zamfara ƙaddamar da

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 

A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci.

Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.”

Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take.

Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka.

Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da ta nemi hukunta ma’aikatan jinya, masu koyon aiki ko na wucin gadi saboda shiga yajin aikin.

Ta ce dukkan mambobinta sun yi amfani da ‘yancinsu na yajin aiki bisa doka.

Ƙungiyar ta yaba da goyon baya da haɗin kai da mambobinta suka nuna a lokacin yajin aikin na kwanaki bakwai, wanda aka fara a ranar 29 ga watan Yuli, 2025.

Yajin aikin ya haifar da tsaiko sosai ga ayyukan jinya a asibitocin gwamnati a faɗin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 
  • HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
  • Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya  
  • Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta 
  • Tinubu Ya Cika Alƙawurran Da Ya Ɗauka – Ƙungiyar Gwamnonin Arewa
  • Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC
  • Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
  • Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
  • ‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu 
  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta