Daga Taklimakan Zuwa Sahara: Karin Abubuwan Al’ajabi Na Faruwa Bisa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Yaki Da Kwararar Hamada
Published: 17th, June 2025 GMT
Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. A zamanin yanzu, kasar Sin ba kawai take jin dadin sauye-sauyen da ke faruwa a sassan hamada na kasar ba, hatta ma tana fatan ganin karin yankunan hamada sun zama dausayi a fadin duniya. Don haka, take kokarin bayar da fasahohinta ga kasashen Afirka da su ma suke fuskantar kalubalen kwararar hamada.
Daga Taklimakan zuwa Sahara, karin abubuwan al’ajabi na ci gaba da faruwa bisa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin yaki da kwararar hamada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC.
Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin KwayaAn bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano, da kuma digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci, inda ya ƙware a ƙirƙire-ƙirƙiren sana’o’i. Ya taɓa jagorantar ɓangaren bincike na musamman a ICPC, tare da sa aiki a fannin sa ido kan ayyukan mazabun ‘yan majalisa.
Har yanzu dai naɗin na jiran tantancewa da amincewar Majalisar dokokin Jihar Kano. A wani bangare, gwamna Abba Yusuf ya yabawa Barr. Muhuyi bisa jajircewarsa da gaskiya a lokacin da yake jagorantar hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp