Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni
Published: 6th, March 2025 GMT
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar.
Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin sunayen ’yan takara za su gudana daga ranar 25 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, 2025.
Shugaban ya ce, za a maido da jerin sunayen ’yan takarar da aka tura musu daga ranar 3 zuwa 10 ga Afrilu yayin da za a wallafa bayanan ’yan takarar daga ranar 11 zuwa 18 ga Afrilu, 2025.
Ya ƙara da cewa an shirya tattara fom ɗin tsayawa takara a ranar 19 zuwa 26 ga Afrilu yayin da jam’iyyun siyasa za su gabatar da fom ɗin takara daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu, 2025.
Ya ce, za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen daga ranar 27 ga watan Mayu har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2025.
Imam ya tabbatar wa jam’iyyun siyasa matakin da za a yi na gudanar da zaɓuka cikin ’yanci, gaskiya da adalci bisa wasu dokoki da jagororin gudanar da zaɓukan kansiloli.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League.
Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4.
Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar Christopher MusaReal Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar.
Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar da kusan Yuro miliyan 200 ga ƙungiyoyin da suka shiga.
A nata martanin hukumar UEFA ta dage cewa wannan sabon hukuncin ba ya nufin an dawo ko an amince da a buga gasar Super League ba ne.