Sin Ta Yi Kira Ga Iran Da Isra’ila Su Dauki Matakan Dakile Ruruwar Wutar Rikicinsu Nan Da Nan
Published: 16th, June 2025 GMT
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Game da halin da ake ciki yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, Guo Jiakun ya ce, ministan wajen Sin Wang Yi ya riga ya tattauna ta waya tare da takwarorinsa na Iran da Isra’ila, inda ya yi kira ga bangarorin biyu su warware rikicin ta hanyar tattaunawa.
Game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu da za a gudanar ba da jimawa ba, Guo Jiakun ya ce, shugabannin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su tsara hadin gwiwa a nan gaba tare, da inganta gina al’umma mai makoma ta bai-daya ta kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya mai inganci.
Game da batun zamowar kasar Vietnam kawar kungiyar BRICS, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin na maraba da Vietnam ta zama kawar BRICS, kuma ana ganin cewa, Vietnam za ta ba da gudummawa mai kyau ga tsarin BRICS.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Guo Jiakun ya
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA