FCCPC Ta Sammaci Air Peace Kan Rashin Maido Da Kuɗin Tikitin Jirgin Da Aka Soke Tafiyarsa
Published: 16th, June 2025 GMT
FCCPC ta lura cewa, waɗannan sassan dokar suna kare ‘yan Nijeriya daga “rashin adalci, rashin sanin ya kamata, daga kwastomominsu.”
A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a gaban hukumar a hedikwatar ta Abuja a ranar Litinin 23 ga watan Yuni 2025.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa, rashin bin wannan umarni na iya haifar da tsauraran takunkumai da suka hada da tara da ɗauri kamar yadda aka bayyana a sashe na 33(3) na dokar.
Har yanzu Air Peace ba ta amsa sammacin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.
Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna.
Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasaA cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.
Wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar ta ambato ministan yana cewa “amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100.”
A 2024 Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau ɗin.
Kazalika, ministan ya ce Gwamnatin Tarayyar ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na Jihar Borno zuwa garin Aba na Jihar Abiya.
“Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai,” in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.