Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro
Published: 19th, June 2025 GMT
Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi.
A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF).
Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar.
Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar.
Taron na gaggawa na zuwa ne a daidai lokacin da tsaro ke taɓarɓarewa a sassa da dama na ƙasar, lamarin da ke ƙara haifar da kira daga al’umma da shugabanni domin ɗaukar matakin gaggawa da haɗin gwiwa tsakanin jihohi da Gwamnatin Tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yansandan Jihohi Gwamnonin APC Matsalar Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19
NiMet ta ce duk wanda ke zaune a wuraren da ruwa ke taruwa ko wuraren da aka bayyana yana da haɗari da su koma wuri mafi aminci.
An kuma shawarci jama’a da su tanadi kayan gaggawa kamar abinci mai yawa da ruwa da kayan taimakon gaggawa da fitila da na’urar adana lantarki ta ‘power bank’.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp